A je a dawo mu na tare da Atiku, Tauraron ‘Dan wasan fim ya kunyata magoya-bayan Tinubu

A je a dawo mu na tare da Atiku, Tauraron ‘Dan wasan fim ya kunyata magoya-bayan Tinubu

  • Mr Ibu ya jaddada goyon bayansa ga jigon jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar idan zai yi takara a 2023
  • Idan har Atiku zai nemi kujerar shugaban kasa, shi Mr. Ibu zai zaba, ba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba
  • ‘Dan wasan kwaikwayon ya bayyana cewa ba zai yi watsi da Atiku, ya rungumi Bola Tinubu ba

Shahararren ‘dan wasan Nollywood, John Ikechukwu Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu, ya yi watsi da jita-jitar da ake yi a kansa game da zaben 2023.

John Ikechukwu Okafor ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram, yace rade-radin cewa ya bi jirgin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sam ba gaskiya ba ne.

PM News ta rahoto John Ikechukwu Okafor yana cewa ya halarci taron marawa Bola Tinubu baya ne saboda wasu da su ke neman taimakonsa sun gayyace shi.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya fadawa Shugabanni yadda za a samu zaman lafiya

‘Dan wasan barkwancin yace babu abin da zai sa ya juyawa abokinsa, tsohon mataimakin shugaban kasa (Atiku Abubabakar) baya, bayan ya taimake sa.

Mista Ibu yace ya yi aiki da Wazirin Adamawa a jiharsa, kuma idan har ya nemi takarar shugaban kasa a karkashin PDP a zaben 2023, lallai zai mara masa baya.

‘Dan wasan fim
Mr. Ibu tare da Atiku Abubakar Hoto: Mandy News
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Mr. Ibu a bidiyo

“Mutane sun same ni domin mu shiga yakin neman zaben Tinubu, ni mutum ne mai cikakkiyar ‘yanci. Duk abin da za ayi a fili, dole a sanar da ni a kan shi.”
“Ban san meyasa abubuwa su ke tafiya haka ba. Amma ban taba zama a kan katanga ba, kullum ina tare da Atiku wanda ya taimake ni ta hanyoyi da dama.”
“Idan zai nemi takarar shugaban kasa, babu shakka Atiku ne ‘dan takara ta.” – Mr. Ibu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue: Ubangiji ne ya zo min yace na sake tsayawa takarar gwamna

Atiku kusan uba ne ga Mr. Ibu

“Atiku tamkar Uba yake a wuri na, na yi masa aiki har a jiharsa, saboda haka ba zan yi watsi da shi ba.
"Ba na kokarin bata Tinubu, amma ba shi ne ‘dan takarata ba, Atiku ne ‘dan takarata.” – Mr. Ibu.

A karshe jarumin yace duk taron da ya halarta ziyara ce saboda an nemi taimakonsa. Hakan bai nufin ya ci amanar mai gidansa, yace Allah ya ba mai rabo sa’a.

Tsofaffin 'yan takara su bada wuri a 2023

A lokacin da wasu ke neman matashin ‘dan takara, ya tsaya takara a 2023. ‘Yan PDP na Arewa ta tsakiya su na rokon Bukola Saraki ya fito takarar Shugaban kasa.

Kungiyar matasan Arewa ta Concerned Northern Youth Forum ba ta goyon bayan dattijo ya karbi shugabancin Najeriya a 2023, tace a bar mulki ga masu jini a jika.

Kara karanta wannan

Gwamnan Nasarawa: APC bata shirya faduwa a 2023 ba, muna da shiri mai kyau

Asali: Legit.ng

Online view pixel