Zaɓen Anambra: Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC ya bayyana dalilin da yasa ya jefa wa Soludu ƙuri'arsa

Zaɓen Anambra: Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC ya bayyana dalilin da yasa ya jefa wa Soludu ƙuri'arsa

  • Dan takarar gwamna na jam'iyyar ADC, Akachukwu Nwankpo, ya jefa wa dan takarar APGA, Charles Soludo kuri'arsa
  • Nwankpo ya bayyana cewa ya tuntubi matasan mazabarsa kafin daukan matakin kuma ya ce ya yi hakan duba da cewa bisa alamu ba zai kai labari ba
  • Dan takarar na ADC ya kara da cewa don kashin kansa ya dauki matakin ma'ana ba uwar jam'iyyar ADC ta umurci ya yi hakan ba

Anambra - A wani lamari da bai cika faruwa ba a siyasa, daya daga cikin abokan fafatawar Farfesa Chukwuma Soludo ya jefa masa kuri'a a karashen zaben gwamnan Anambra a karamar hukumar Ihiala.

Akachukwu Nwankpo, dan takarar gwamna na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), ya ce ya jefa wa jam'iyyar abokin fafatawarsa na All Progressives Grand Alliance (APGA) kuri'arsa.

Read also

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

Yanzu-Yanzu: Ɗaya daga cikin 'yan takarar gwamna ya jefa wa Soludo ƙuri'a a Anambra
'Daya daga cikin 'yan takarar gwamna ya jefa wa Soludo ƙuri'a a Anambra. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Talata bayan kada kuri'arsa.

Karamar hukumar Ihiala ne za ta raba gardama a zaben da aka ce bai kammalu ba a ranar Litinin.

Soludo yana kan gaba da tazara mai yawa a kananan hukumomi 18 na jihar ta Anambra.

Dalilin da yasa na jefa wa Soludo kuri'a ta, Nwankpo

Nwankpo ya ce ya yanke shawarar jefa wa dan takarar APGA kuri'arsa ne saboda jam'iyyarsa ba za ta kai labari ba kamar yadda suka tsara kamar yadda ya zo a rahoton Daily Trust.

A cewar Nwankpo, wanda ya kada kuri'arsa a mazabar Umuapani a akwatin zabe mai lambar 004, Okija, ya ce ya tuntubi matasan Ihiala kafin ya zabi APGA, wanda ya ce bisa dukkan alamu ita zata ci zaben.

Read also

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

Da aka tambaye shi ko jam'iyyar ADC ta goyi bayan abin da ya yi, ya ce don kashin kansa ya dauki matakin kuma hakan zai bashi damar bada gudunmawa a gwamnatin APGA karkashin gwamna Willie Obiano.

Ya yabawa jami'an tsaro kan yadda suka tabbatar an yi zaben cikin zaman lafiya, kafin zaben, yayin zaben da bayan zaben.

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.

Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Zaben Anambra: Yau Talata za'a cigaba daga inda aka tsaya, APGA na kan gaba

Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel