An sa ranar da za ayi shari’a tsakanin PDP da ‘Yan siyasan Zamfara da suka koma APC

An sa ranar da za ayi shari’a tsakanin PDP da ‘Yan siyasan Zamfara da suka koma APC

  • A karshe babban kotun tarayya da ke Abuja zai saurari shari’ar PDP da ‘Yan siyasan jihar Zamfara.
  • Alkali Inyang Ekwo yace za a zauna a kan karar a ranar 18 ga watan Junairun shekara mai zuwa.
  • Tun a watan Satumba PDP ta shigar da kara, tana so a sauke Gwamna da ‘Yan Majalisan Zamfara.

Abuja - A ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, 2021, babban kotun tarayya da ke garin Abuja ta sa ranar da za ta saurari karar da jam’iyyar PDP ta shigar.

Jam’iyyar hamayya ta PDP tana karar gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle a kan sauya-sheka da ya yi, zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

The Nation tace PDP tana so a sauke duka sauran ‘yan majalisun Zamfara da suka sauya-sheka.

Read also

Shugaban kasa a 2023: Matasan arewa sun nuna goyon bayansu ga shahararren dan siyasar kudu

PDP ta shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/650/2021 ta hannun lauyanta, James Onoja tun Satumba. Sai bayan wata daya aka sa lokacin da za a zauna.

Yaushe za a fara zama a kotu?

Sai a shekara mai zuwa za a fara yin shari’ar. Alkali Inyang Ekwo ya sa 18 ga watan Junairun 2022 a matsayin ranar da za a saurari karar da aka shigar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matawalle
Gwamna Bello Matawalle da Buhari Hoto: africannewstoday.com
Source: UGC

An shaidawa James Onoja SAN cewa an daga karar sai watan Junairu mai zuwa domin a zauna. Duka bangarorin sun samu labarin sabon ranar da kotu ta sa.

Jaridar The Eagle tace karar za ta shafi Sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da duk ‘yan majalisar jihar. Har yanzu mataimakin gwamnan jihar bai bar PDP ba.

Babban lauya Mike Ozekhome SAN wanda ya tsayawa sauran wadanda ake tuhuma, ya tabbatar da cewa ya samu labarin sa ranar da Inyang Ekwo ya yi a jiya.

Read also

Dan Shekara 25 a matsayin shugaban matasan PDP: Martanin 'yan Najeriya

Lauyoyin PDP suna so kotu ta fassara masu abin da sassa na 1(2), 188, 287, 221, 177(c), 106(d) da 65(2)(b) na tsarin mulkin 1999 suka ce game da sauya-sheka.

Hukumar dillacin labarai na kasa tace a ranar 15 ga watan Oktoba, 2021, jam’iyyar adawar ta hada da Sanatocin Zamfara da ‘yan Majalisa 27 a cikin karar ta su.

James Onoja SAN ya je kotu

Idan za ku tuna a ranar Juma’a, 15 ga watan Oktoba, 2021, jam’iyyar PDP ta kai kara, tana so a sauke masu rike da mukamai a jihar Zamfara da suka sauya-sheka.

Jam’iyyar hammayar tana so a tsige gwamna Bello Matawalle, duka Sanatocin jihar uku da kuma ‘yan majalisa 30 da suka shiga jirgin APC a tsakiyar shekarar nan.

Source: Legit.ng

Online view pixel