Gwamnonin Yarbawa sun ce jigon APC, Bola Tinubu zai iya rike Gwamnatin Najeriya

Gwamnonin Yarbawa sun ce jigon APC, Bola Tinubu zai iya rike Gwamnatin Najeriya

  • Gwamnonin Kudu maso yamma sun gana da Bola Tinubu a jihar Legas
  • Rotimi Akeredolu ya jagoranci gwamnonin bayan taron da suka shirya
  • Shugaban gwamnonin yankin ya yabi babban jagoran na jam’iyyar APC

Lagos - Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya, Rotimi Akeredolu (SAN), yace Asiwaju Bola Tinubu zai iya jan ragamar kasar nan.

Mai girma gwamnan jihar Onso, Rotimi Akeredolu ya yabi tsohon gwamna Asiwaju Bola Tinubu a lokacin da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Legas.

Jaridar Vanguard ta rahoto Rotimi Akeredolu yana yabon Bola Tinubu wanda ya yi gwamna a Legas tsakanin 1999 da 2007, yanzu babban jigo a APC.

A cewar shugaban kungiyar gwamnonin na jihohin kudu maso yamma, Bola Tinubu yana yi wa yankin bakin kokarinsa na ganin ya jagoranci al’ummarsa.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar Yarbawa ta tsaida ‘Dan takararta tilo a zaben Shugaban kasa daga APC

Gwamna Akeredolu ya yi jawabi ne a madadin sauran abokan aikinsa da yake zantawa da ‘yan jarida a unguwar Bordillion, birnin Ikeja a ranar Talatar nan.

Gwamnan na jihar Ondo yace sauran gwamnonin yankin Yarbawa sun yi amanna da jagorancin Bola Tinubu wanda da kokarinsa aka kafa jam’iyyar APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnonin Yarbawa
Wasu Gwamnoni tare da Bola Tinubu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Punch ta rahoto Akeredolu yana cewa Tinubu ba jagora ba ne a iyaka yankin kudu maso yammacin Najeriya, jagora ne na jam’iyyar APC a fadin kasa.

Dr. Kayode Fayemi ya janye jikinsa a Bordillion

Abin da ya ba mutane mamaki shi ne yadda gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ya yi mim-ara-koma-baya a wajen wannan zama duk da yana Legas.

Kayode Fayemi ya halarci taro da sauran takwarorinsa, amma ba a gan shi a gaban gidan Tinubu ba. Jaridar Parrot Nigeria ta fitar da wannan rahoton dazu.

Kara karanta wannan

Gwamnonin kudu sun gana a jihar Legas, Sun cimma matsaya kan abubuwa da dama

Me ya kai su gidan Bola Tinubu?

“Mun yi taron gwamnonin Kudu maso yamma. Bayan zaman sai muka ga bukatar mu zo, mu kawo wa jagoranmu ziyara wanda ya dawo gida kalau.”
“Mun zo nuna masu soyayyar da mu ke yi masa, kuma mu godewa Allah a madadinsa. Yana ta karbar baki, gidansa ya zama Makka.” - Akeredolu.

Tinubu ne zabin Yoruba Welfare Group

A jiya kungiyar Yoruba Welfare Group ta fito da tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu a matsayin ‘Dan takarar ta na shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Masu hasashen siyasa suna ganin tsohon Gwamnan na Legas zai nemi mulki a zabe mai zuwa. Tinubu zai iya fuskantar kalubale na gaske tun daga APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel