MURIC ta bada sunayen Tinubu, Musulman Yarbawa 7 da za su iya zama Magadan Buhari

MURIC ta bada sunayen Tinubu, Musulman Yarbawa 7 da za su iya zama Magadan Buhari

  • Muslim Rights Concern ta koka da yadda ake tauye Musulman Yarbawa a siyasa
  • Kungiyar MURIC tace Obasanjo, Shonekan da Osinbajo sun shiga fadar Aso Rock
  • Hakan ta sa a 2023, MURIC take so a samu Musulmi ya zama shugaban Najeriya

Nigeria - Kungiyar addinin muslunci ta Muslim Rights Concern wanda aka fi sani da MURIC, ta tsoma baki game da siyasar da wanda za a ba mulki.

MURIC ta fitar da jawabi a ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, 2021, tana bayyana sha’awarta na ganin an samu Bayarabe kuma musulmi a kan mulki.

A jawabin da kungiyar ta fitar, Punch ta rahoto shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola yana cewa musulmin kudu maso yamma bai taba mulki ba.

Farfesa Ishaq Akintola ya ambaci sunayen wasu ‘yan siyasa da suka fito daga Kudu maso yamma da za su iya karbar shugabancin kasar nan a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Shugaban NHRC da sauran manyan lauyoyi 71 da suka samu girmamawa ta SAN

Akintola ya yi wa jawabin na sa take da; ‘2023: On Yoruba Muslim presidential candidate we stand’, yana bayanin matsayar MURIC game da zaben.

Tinubu, da Aregbe
Tinubu da Aregbesola Hoto: nationaldailyng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a dama wa da Musulmanmu - MURIC

A lokacin da an samu kiristoci uku daga kasar Yarbawa da suka zama shugaban kasa ko mataimakin shugaba a kasar nan, babu musulmi ko daya.

Olusegun Obasanjo ya zama shugaban kasa sau biyu a (1976–79) da (1999 -2007). Earnest Shonekan ya yi rikon kwarya, yau Yemi Osinbajo na mulki.

Kungiyar addinin ta ambaci Bola Tinubu, tace a daina tauye wa musulman yankin hakkinsu.

'Yan takarar 2023?

Ga jerin wadanda za su iya yin takarar shugaban kasa a cewar kungyar MURIC:

1. Bola Tinubu – Tsohon Gwamnan Legas

2. Muiz Banire – Tsohon mai ba APC shawara a kan harkar shawara

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya karyata rade-radin barin jam'iyyar PDP da tsayawa takarar shugaban kasa

3. Farfesa Ishaq Oloyede – Shugaban hukumar JAMB

4. Dr. Kadiri Obafemi Hamzat - Gwamnan jihar Legas

5. Babatunde Fashola – Minista, Tsohon Gwamnan Legas

6. Rauf Aregbesola – Minista, Tsohon Gwamnan Osun

7. Fatai Buhari – Sanatan jihar Oyo

8. Dr. AbdulLateef AbdulHakeem – Tsohon Kwamishinan Legas

ABUSITES da suka zama Gwamnonin jihohi

A karshen makon da ya gabata ne mu ka kawo jerin wasu Gwamnonin jihohin masu-ci da suka yi karatu a jami’ar ABU Zaria a lokacin da suke neman ilmin boko.

Daga 2015 zuwa 2019, akwai ABUSITES 7 da suka zama Gwamnoni a kasar nan. A shekaru 23, tsofaffin daliban jami'ar sama da 30 ne suka hau kujerar gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel