‘Yan wasan Kannywood sun kirkiri fim a kan rikicin Boko Haram a Arewacin Najeriya

‘Yan wasan Kannywood sun kirkiri fim a kan rikicin Boko Haram a Arewacin Najeriya

  • Falalu A. Dorayi ya shirya wasan kwaikwayo a game da rikicin Boko Haram
  • Mutane sun yaba da gwanintan da aka nuna a wannan fim mai suna Musababbi
  • Gajeren wasan mai tsawon mintuna 15 ya nuna yadda aka rika yaudarar matasa

Kano - Fitaccen mai bada umarni a Kannywood, Falalu A. Dorayi, ya shirya wani wasan fim da ya nuna tarihin kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram.

A wannan fim mai suna Musababbi, Falalu A. Dorayi ya nuna yadda ‘yan ta’addan suka rika rudar matasa da kudi har suka shiga cikin mummunar tafiyar.

Kamar yadda shafin Kannywood ya wallafa a Facebook, an fitar da wannan gajeren wasan kwaikwayo a ranar Lahadi, 17 ga watan Oktoba, 2021.

‘Yan ta’addan suna jawo mutane da sunan za suyi aikin Allah. Sannan jagororin ‘yan ta’addan sun rudi jama’a da baiwar haddace Al-Kur’ani mai tsarki.

Read also

Gwamnatin Tarayya tana biyan malaman jami’a N6, 000 rak a matsayin albashin karshen wata

A bidiyon za a fahimci yadda ‘yan ta’addan ke yi wa matasa barazana, da kuma rawar da malamai na gaskiya suke taka wa wajen fadakar da al’umma.

Har ila yau, fim din ya nuna kokarin da jami’an tsaro suke yi wajen kare rayuka da dukiyar al’umma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jarumin Kannywood
Falalu A. Dorayi Hoto: www.northernwiki.com
Source: UGC

Wadanda suka shirya wasan kwaikwayon

Falalu A. Dorayi ne ya bada umarni kuma ya bada labarin, yayin da Sani Ali Abubakar wanda aka fi sani da Indomie ne ya dauki nauyin shirya wasan.

Sauran wadanda suke taimaka wajen shirya wasan Musabbabi su ne Sanusi Danyaro, Abdulmumuni Pananais, Jimo Yakubuu da Abdul A.P.

Martanin Audu Bulama Bukarti

Audu Bulama Bukarti ya yabi wannan fim mai tsawon mintuna kusan 15, yace darektan ya yi matukar kokari wajen fadakar wa a kan Boko Haram.

Malam Bulama Bukarti wanda masani ne a kan sha’anin tsaro a yankin Afrika, yace inda aka shirya wasan ya yi kama da sansunan ‘yan ta’addan.

Read also

Watanni 4 da sauya-shekar gwamna zuwa APC, PDP tace ana neman rusa mata hedikwata

“Wannan sabon shirin mai suna "Musabbabi" na Falalu A. Dorayi gajere ne (14 minutes), amma yayi matuqar kokari wajen haska yadda 'yan Boko Haram ke yaudarar matasa da addini da kuma kudi.”
“Gurin da aka dauka yayi kama da sansanin 'yan Boko Haram. Kuma an nuna matuqar kwarewa wajen daukar hoto da sauti masu kyau. Kuma wallahi gemun Falalu da asuwakinsa sunyi kama da na…”

Society for Arewa Development ta yi taro

A makon da ya gabata aka ji Society for Arewa Development ta yi zama domin murnar samun ‘yancin kai. A wajen zaman, an yi magana kan rashin tsaro.

Kungiyar ta tattauna game da halin da yankin Arewacin Najeriya yake ciki yau. A karshen zaman, an bada shawara ayi zama domin a samu zaman lafiya.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel