Gwamnatin Tarayya tana biyan malaman jami’a N6, 000 rak a matsayin albashin karshen wata

Gwamnatin Tarayya tana biyan malaman jami’a N6, 000 rak a matsayin albashin karshen wata

  • Wasu malaman Jami’a suna kukan cewa ba a biyansu hakkokinsu da kyau
  • Akwai malaman da suka yi ikirarin N6000 kacal aka biya su a karshen wata
  • Ofishin babban akawun gwamnatin yace kungiyar ASUU ce ta jawo wannan

Abuja - Ofishin babban akawun gwamnatin tarayya, ta maida martani game da koke-koken da ake yi na cewa malaman jami’a na fuskantar matsalar albashi.

Babban akawun gwamnatin Najeriya ya yi magana ne bayan samun labarin malamai musamman daga jami’ar UNIMAID ba su samun albashinsu da kyau.

Gwamnatin tarayya tace abin da ya faru shi ne malaman jami’ar sun makara wajen bada takardunsu a lokacin da ake tattara bayanai game da ma’aikatan jami’a.

Jaridar Daily Trust ta rahoto OAGF yana cewa bayan rashin bada bayanan a kan-kari, malaman jami’ar Maiduguri sun bada bayanan da ba na gaskiya ba.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Sai Majalisa ta kawo dokar hana yaran mala’u yin Digiri a Jami’o’in waje - ASUU

Darektan kula da sha’anin IPPIS na ofishin AGF, Dr. Nsikak Ben yace laifin malaman jami’an ne, domin tun farko su da kansu, suka jefa kansu a wannan matsala.

Idris Ahmed
Akawun gwamnatin Najeriya, Ahmed Idris Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku kuka da kanku - OAGF

“Maganar rashin biyan wasu daga cikin ‘yan kungiyar malaman jami’an na ASUU albashi laifinsu ne, saboda ba su yi rajistar daukar bayanai ba.”
“Ko lokacin da gwamnatin tarayya tace a tattara bayanan ‘yan ASUU, wasu ba su yi rajistar ba, wasu jami’o’in sun kawo bayanan bogi a na’urorinmu.”
“Jami’ar Maiduguri da Umudike ba su kawo bayanansu a watan Maris, 2020 ba, ko da suka kawo daga baya, ba bayanan kwarai suka kawo ba.” – Dr. Ben.

A wani sako da ya aika wa manema labarai, Nsikak Ben yace an yi tanadi ta yadda za a karbi koken ‘yan kungiyar ASUU a wuraren aikinsu, domin a gyara.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Shekarau ya bayyana makasudin kai korafin Ganduje gaban Shugabannin APC na kasa

Darektan yake cewa akwai sama da ma’aikatun tarayya 700 a manhajarmu, idan kungiyar ASUU kadai ta ke kukan rashin biyan albashi, kai ma dai ai ka fada.

A yau ake jin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari tayi kasafin biliyoyin kudi domin hukumomi su san duk abin da jama’a suke yi a wayoyinsu da kaar WhatsApp.

Kungiyar nan ta SERAP tace babu dalilin da zai sa jami'an Gwamnati su san sirrrin Jama’a. Hakan ya sa kungiyar ta kai kara zuwa babban kotun tarayya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel