Budurwa Ta Sace Zuciyar Mahaifin Tsohon Saurayinta Bayan Raba Jiha Da shi

Budurwa Ta Sace Zuciyar Mahaifin Tsohon Saurayinta Bayan Raba Jiha Da shi

  • Wata budurwa ta jawo kace-nace bayan ta saki wani video dake nuna yadda take soyayya da mahaifin tsohon saurayinta
  • A wasu jerin gwanon rubutu da ta wallafa, ya nuna yadda take murna, ta ce yafi bata nishaɗi akansa
  • Budurwar ta ce, mutane suna tunanin ita da tsohon saurayin nata suna tare ne har yau, amma tuni suka raba gari duk da ana mugun tare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ba haka aka so ba, wai ƙanin miji yafi miji kyau.

A wannan gwadaben, ba haka aka so ba yayin da wasu wata budurwa ta rabu da wani matashi, ta kama soyayya da mahaifinsa.

Matar da ta bayyana haka, tace ita tafi farin ciki da tsohon hannun fiye da yaron da suka soma soyyayya a farkon fari.

Tiktok
Budurwa Tayi Kuri Ga Tsohon Saurayin ta Bayan Sun Rabu Dashi Ta Sace Zuciyar Tsohon Sa Hoto: Tiktok
Asali: TikTok

Matashiyar tace tunda ta soma tsinkar fure da baban saurayin nata, duniya ta koma mata sabuwa fil. Tace, duk da haka, basu samu saɓani da tsohon saurayin nata ba domin suna ci gaba da zaman mutunci kamar yadda aka saba.

Kara karanta wannan

“Uwar Miji Ta Ce Ba Zan Taba Haihuwa Ba”: Yar Najeriya Ta Samu Cikin Yan 3, Ta Nuna Wa Duniya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matar tace, duk da cewa sun dade da rabuwa a fagen soyayya, mutane da yawa tunani suke har yanzu suna tare, kuma suna son juna su.

A Bidiyon data wallafa a Tiktok, tayi wani gajeren rubutu dake faɗin:

"Yayin da mutane ke tunani kana tunanin soyayya ɗan mai gidan ka (Tsohon Saurayin).
"Kunga nafi farin ciki da mahaifin sa, amma kuma tamu tazo ɗaya nida shi ...Kowa yana maraba da alaƙar," In ji ta.

A kalamanta:

"Kawai sai na yanke hukuncin auren mahaifinsa saboda gudun ɓacin zuciya da kuma gudun fushin besty , kamar yadda mawakiya Nicky Minaj take yawan bamu shawara"

Kafar Sada Zumunta na Zamani Sun Maida Martani Cike da Mamaki

Damola ta ce:

"Waiiii! Wani Fim waishi "Matar Uba" dana kalla ya zama gaskiya yau".

Sanie ya ce

Kara karanta wannan

Hazikin Matashi Dan Najeriya Ya Sace Zuciyar Kyakkyawar Budurwa Cikin Minti 5, Hirarsu Ta Bada Mamaki

"Shugaba, jagora, kuma shugabar mata, uwagijiyar mu, mai jan ragamar mata kuma shugabar ƙasa ta mata, mun yarda mun amince da ke".

Hilda-yego20 ta ce:

"Idan har kayi mun rashin adalci a soyayya, to kasani zan nemi soyayyar mahaifin kane. A kula da batun nan".

Jennirose ta ce:

"Yaya kike ji yayin da kike ganin sa kullum kusa dake, ko baku taɓa keɓewa dashi bane yayin da kuke soyayya."

Mimxx_xx06 ta ce:

"Kayyasa!!! Nasan zan iya haka Nima. amma kada ka taɓa bari hukuncin mutane akan na yayi tasiri gare ka".

Belle cike da mamaki ta ce:

"Sadaukiyar yaƙi, mai nasara, zakanya ta iso!!!

Andrea Charlotte ta fusata ta ce:

"Idan har ka taɓa cuta ta a soyayya, tabbas ina zuwa gare ka domin yin aoyagyayda mahaifin ka," in ji ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel