Garin Sauri Don Kada a San Ta Yi Dare a Waje: Budurwa Ta Yi Kicibis Da Iyayenta a ‘Go-Slow’

Garin Sauri Don Kada a San Ta Yi Dare a Waje: Budurwa Ta Yi Kicibis Da Iyayenta a ‘Go-Slow’

  • Wani bidiyo mai ban dariya na wata matashiya da ta hadu da iyayenta a cunkoson ababen hawa a Lagas ya yadu a TikTok
  • Matashiyar na cikin motar tasi tana sauri ta isa gida don kada iyayenta su gane cewa ta yi dare a waje
  • Sai dai, ta yi kicibis da su a 'go slow', sannan bayan sun gaisa sai ta tambaye su ko za ta iya dawowa cikinsu

Lagos - Wata matashiyar budurwa ta wallafa wani bidiyon ban dariya da ke nuna lokacin da ta yi kicibis da iyayenta a cunkoson ababen hawa a Lagas.

Matashiyar na sauri ta isa gida kasancewar ta jima a waje kuma ya kamata ace ta koma gida da dadewa.

Budurwa da iyayenta a mota
Garin Sauri Don Kada a San Ta Yi Dare a Waje: Budurwa Ta Yi Kicibis Da Iyayenta a ‘Go-Slow’ Hoto: @yourdramaqueen
Asali: TikTok

Ta dauki hayar motar tasi

Abun takaici, sai 'go slow' ya kama su a hanya kasancewar a Lagas suke, ana haka ne sai ta lura da motar iyayenta a daya bangaren kusa da ita suma dai cunkoson ya ritsa da su a hanyarsu ta komawa gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yanke shawarar yin bidiyon yadda haduwarsu ta kasance yayin da take ta dariya.

Ta bayyana yadda iyayen nata suka kama ta a 'go slow' lokacin da ya kamata ace tana gida.

Matashiyar ta tambayi iyayenta ko suna da sarari a motarsu don ta shiga su rage mata hanya; don su dan kashe lokaci tare a 'go slow' tare da shan hira kafin su isa gida.

Iyayenta sun ki, sannan mahaifiyarta tace tana iya shigowa idan za ta yi manejin rike saman kofar.

Kalli bidiyon a kasa

Jama'a sun yi martani

@crypto_arena101 ta ce:

"Menene dalilin da yasa kike fada mana?"

@kelzmnny ta yi martani:

"Kalli yadda iyalin suka hadu."

@heis_wizdom ta ce:

"Haduwar iyali."

@clara76476 ta rubuta:

"Gaskiya akwai dadin kallo."

@kehinde0915 ya rubuta:

"Ina iya hango tsantsar farin cikin da kike ciki."

@birohen ya yi martani:

"Kin hadu a wannan bidiyon yarinya."

@the_only_theo ta rubuta:

"Awwwwwwww."

@tosnice ta yi martanmi:

"Idan suka kwace maki wayarki a 'go slow' yanzu sai ki yi ta kuka...muna ci gaba da sanya ido."

Bidiyon karamar yarinya tana tuka tuwo ya ba da mamaki

A wani labari na daban, jama'a sun jinjinawa wata karamar yarinya bayan sun ci karo da bidiyonta tana tuka tuwo sai kace wata babba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel