Ban taɓa sanin muna da kuɗi ba sai da na kai shekara 13: Davido ya magantu kan zuhudun mahaifinsa

Ban taɓa sanin muna da kuɗi ba sai da na kai shekara 13: Davido ya magantu kan zuhudun mahaifinsa

  • Fitaccen mawakin Najeriya, Davido, ya yi karin haske game da irin daular da ya taso cikin ta yayin wata hira da aka yi da shi
  • Mawakin, wanda a baya-bayan nan ya yi wa marayu kyautan miliyan 250 ya ce bai taba sanin mahaifinsa attajiri bane sai da ya kai shekara 13
  • Davido ya bayyana cewa mahaifinsa wanda biloniya ne Honda Accord ya ke tuka wa a wannan lokacin ita ma mahaifiyarsa mota mara tsada ta ke hawa

Fitaccen mawakin Najeriya, Davido, ya yi magana a kan mahaifinsa, Adedeji Adeleke da arzikin da suke da shi yayin wata hira da aka yi da shi a kwanan nan da ta bazu a intanet.

Mawakin wanda ya lashe kyaututuka da dama ya fere biri har wutsiya a hirar da ya yi da EarnYourLeisure inda ya ce bai taba sanin mahaifinsa na da kudi ba da farko.

Kara karanta wannan

Mota ta farko da zan hau ni zan kera ta : Yaron Najeriya da ya hada mota da karafuna

A cewar Davido, mahaifinsa mutum ne mai saukin kai kuma baya facaka da kudi ga shi ba shi da girman kai ko a harkar kasuwancinsa.

Ban taba sanin muna da kudi ba sai da na kai shekara 13: Davido ya magantu kan zuhudun mahaifinsa
Davido ya yi magana kan irin rayuwa mai sauki da mahaifinsa ke yi duk da shi biloniya ne. Hoto: Davido
Asali: Instagram

Davido ya kuma ce bai ma taba sanin mahaifinsa hamshakin mai kudi bane har sai da ya kai kimanin shekara 13 saboda suna rayuwa ne irin ta kowa da kowa. Ya ce mahaifinsa duk da biloniya ne Honda ya ke hawa.

Da ya ke magana a kan mahaifinsa, Davido ya ce:

"Har yau, ba shi da girman kai kuma baya almubazzaranci da kudi, yadda ya ke kasuwancinsa yana birge ni.
"Da na girma har na kai shekara 11, ba na kusanci da mahaifina saboda kullum aiki ke gabansa. Ina iya tuna kullum sai dare ya ke dawo wa gida. Ban san mene ya ke yi ba.

Kara karanta wannan

BaAmurkiya mai digiri 4 ta gangaro Afrika, ta yi wuff da dan achaba, tace hadin Ubangiji ne

"Ban ma san muna da kudi ba har sai da na kai shekaru 13 domin muna rayuwa ce kamar kowa. Shi biloniya ne amma Honda ya ke hawa. Yana da Honda Accord mai launin silver, yana da direba, mahaifiya ta tana da Toyota ko Honda. Suna rayuwa ne kamar kowa har sai da muka koma sabon gidan mu. Muna isa sabon gidan sai na gane cewa lallai 'muna da kudi'."

Kalli bidiyon a kasa:

Arziki baya magana - Masu amfani da intanet sun yi martani

Abin da Davido ya ce game da sassaukar rayuwa da mahaifinsa ke yi duk da shi biloniya ne ya janyo mutane suna ta tofa albarkacin bakinsu a shafukan intanet.

Ga wasu daga cikin abubuwan da mutane ke cewa:

Socialite_htx:

"Arziki baya hayaniya!! Wasu daga cikin mafiya arziki suna hawa motocci marasa tsada. Kowa ya bude idonsa!."

Keishabeeecooks:

"Ka yi shiru ka rika kidaya kudin ka."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yadda wani mutumi ya sayi mataccen gida kan kudi N416m ta yanar gizo

Adavanced_family_medicine:

"Sun bashi tarbiya mai kyau."

Dchevas_skincare:

"Lallai, ni gani ina ta murmushi da dariya, Allah wadan talauci."

Kinsleyemeka:

"Ni da mahaifiyata da dan uwa na muna aiki sosai a gona amma ba na tunanin mu talakawa ne domin mahaifiyata tana bamu duk abin da muke bukata, Allah ya saka mata da alheri."

Thatboy_code:

"@achchristopher_ Ban yar ba. Sai dai zai iya zama gaskiya saboda yaro ne shi a lokacin don haka ba zai sani ba. "

Asali: Legit.ng

Online view pixel