Sowore Ya Cire Tsoro, Ya Nuna Yatsa ga Ministan Tinubu a Abuja

Sowore Ya Cire Tsoro, Ya Nuna Yatsa ga Ministan Tinubu a Abuja

  • Fitaccen mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Omoyele Sowore, ya tunkari Ministan Ayyuka, David Umahi, a hedkwatar ‘yan sanda ta Abuja
  • Sowore ya gamu da Umahi a ofishin yan sanda a lokacin da Ministan ke kokarin warware wani batu da matar auren da ke zarginsa da zaluntarta
  • Ma’aikatan Ministan sun yi yi kokarin ture Sowore, amma dan gwagwarmayar ya tsaya da kafarsa tare da zargin Ministan da amfani da karfi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Omoyele Sowore, sanannen mai rajin kare hakkin bil’adama, a ranar Laraba 25 ga watan Fabrairu, 2026 ya tunkari Ministan Ayyuka, David Umahi a caji ofis.

Sun hadu a hedkwatar ‘yan sandan Abuja, kan zargin Ministan na amfani da karfin iko wajen zaluntar wata mata mai suna TracyNither Nicolas Ohiri.

Kara karanta wannan

Dalilai 3 da suka jawo Tinubu ya umarci Sufeton yan sanda ya yi murabus

Omoloye Sowore ya soki Minista David Umahi a ofishin yan sanda
Omoloye Sowore mai fafutukar kare hakkin dan adam Hoto: Omoloye Sowore
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Sowore ya tambayi Ministan dalilin amfani da ‘yan sanda wajen biyan bukatun kansa.

Yadda Sowore ya gamu da Minista a Abuja

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kalaman Sowore sun fusata ma’aikatan Ministan, inda suka shiga fada da shi, wasu kuma na kokarin ture shi.

Ministan, wanda da farko ya gaisa da Sowore daga baya ya murtuke fuska yayin da yake maganganu da ba a ji ba.

Sowore ya zargi David Umahi da nuna iko a kan wata mata
Dabid Umahi, Ministan ayyuka na Najeriya Hoto: David Umahi
Source: Facebook

Sowore ya wallafa bidiyo na abin da ya faru yana mai cewa, a cikin dakin taro, ‘yan sanda sun shirya ba Ministan damar ya yi wa wata matar aure barazana.

Matar mai suna TracyNither na zargin Davide Umahi da hana ta kudin da take binsa, Naira miliyan 250 na tsawon shekaru 12.

An kama TracyNither Nicolas Ohiri a Legas bisa zargin cin zarafi ta yanar gizo sannan aka tura ta Abuja inda aka tsare ta.

Kara karanta wannan

Zargin kashe Kiristoci: Matakai 6 da ake son Trump ya ɗauka a kan Najeriya

Zargin Sowore kan yan sanda

Omoloye Sowore ya bayyana cewa shari'ar ana bin kudi magana ce ta rikicin farar hula amma yana ganin yan sanda ba su dauki lamarin a haka ba.

Ya kara da cewa an dauki maganar kamar ta aikata wani mummunan laifi har suka shirya taro a hedkwatar inda Ministan ya shiga don tsoratar da ita da yi mata wulakanci.

Ministan ya bar wurin cikin fushi, ‘yan sanda kuma ba su ba ta belin wucin gadi ba. Daga baya an ji cewa Umahi ya yi alkawarin cewa ba ta ga komai ba tukuna.

Rundunar yan sanda ko David Umahi ba su fitar da sanarwa a hukumance kan zarge-zargen da Omoyole Sowowre ke yi masu ba.

Sowore ya yi magana kan Minista

A baya mun wallafa cewa Mai rajin kare hakkin dan adam, Omoyele Sowore ya shigar da ƙorafi a gaban Babban Lauyan jihar Florida a kan Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Yaron Sheikh Gumi zai yi takara a Kaduna, ya fadi kujerar da yake hari a 2027

Mai fafutukar kare hakkin dan adam wanda ya shigar da ƙorafin ta hannun lauyansa yana neman a kwace kadarorin da Nyesom Wike ya saya a ɓoye a jihar.

Omoyele Sowore ya zargi Wike da sayen gidaje uku a Winter Springs, Florida da darajarsa ya kai Dala miliyan 6 da kuɗin haram da aka karkatar daga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng