Abin da Atiku Ya Ce bayan Sanin Halin da El Rufai ke Ciki a Kulle a Abuja
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce gwamnati za ta dauki alhakin duk abin da ya samu Nasir El-Rufai
- Atiku ya nuna damuwa kan rahoton zubar jini daga hancin El-Rufai yayin da hukumomin bincike ke ci gaba da tsare shi a Abuja
- Ya bukaci gwamnati ta fayyace hukumar da ke tsare da shi tare da ba da belinsa idan ba za a iya tabbatar da lafiyarsa ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana game da ci gaba da garkame Nasir El-Rufai da ake yi.
Atiku Abubakar ya ce za a kama gwamnatin tarayya da alhakin duk wani abu da ya samu tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a yau Talata 24 ga watan Fabrairun shekarar 2026.
Atiku Abubakar ya magantu kan tsare Nasir El-Rufai
Atiku ya fadi haka ne bayan rahotannin da ke cewa El-Rufai ya yi zubar jini daga hanci yayin da yake tsare, yana mai cewa lamarin abin damuwa ne matuka a cikin tsarin dimokuradiyya.
Ya jaddada cewa lafiya da jin dadin tsohon gwamnan na da muhimmanci ga iyalansa da abokansa, yana mai cewa dole ne a ba ‘yan Najeriya cikakken bayani kan halin da yake ciki.
A cikin sanarwar, Atiku ya ce gwamnati ta fito fili ta bayyana wace hukuma ce ke tsare da shi, ko dai EFCC da ICPC da DSS ko wata hukuma ta tsaro.
Ya ce ‘yan Najeriya na da hakkin sanin gaskiya, domin boye-boye a batun tsare mutane na kara jefa shakku a zukatan jama’a.

Source: Twitter
Shawarar Atiku ga hukumomi kan El-Rufai
Atiku ya kara da cewa duk wacce hukuma ke da alhakin tsare da El-Rufai, tana da hakkin kare lafiyarsa, martabarsa, da ba shi damar ganin iyalansa da lauyoyinsa.
Ya ce idan har hukumomi ba za su iya tabbatar da lafiyarsa da hakkokinsa ba, to abin da ya dace shi ne a ba shi beli ba tare da bata lokaci ba.
A cewarsa, idan wani abu ya samu El-Rufai, gwamnati ce za ta dauki alhakin hakan domin ya shiga hakkinsa na dan Adam.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi zargin cewa ana kara ganin alamun zargin fifita wasu da kuma tsananta wa ‘yan adawa a yaki da cin hanci da rashawa.
Ya ce yaki da cin hanci dole ne ya kasance ba tare da son rai ko nuna bangaranci ba, tare da bin doka ga kowa ba tare da tsoro ko son zuciya ba.
Zarge-zargen malamin Musulunci kan El-Rufai
Mun ba ku labarin cewa malamin addinin Musuluncin nan a jihar Kaduna, Sheikh Halliru Maraya, ya yi zarge-zarge kan Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
Sheikh Halliru Maraya ya yi zargin cewa El-Rufai bai yi wa Kiristoci adalci ba wajen aiwatar da tsarin gwamnatinsa na daina daukar nauyin sauke faralinsu.
Malamin ya kwararo yabo ga Gwamna Uba Sani kan matakin da ya dauka na soke daina daukar nauyin sauke faralin Kiristoci wadanda ke da yawa a Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

