Ramadan: Zakir Naik Ya Jero Abubuwa 25 da za Su Sa Mai Azumi Samun Lada Mai Yawa

Ramadan: Zakir Naik Ya Jero Abubuwa 25 da za Su Sa Mai Azumi Samun Lada Mai Yawa

  • Fitaccen Malamin Musulunci na duniya, Dr Zakir Naik ya yi wa al'ummar Musulmi nasiha game da ayyukan alheri da ya kamata su yi a Ramadan
  • A nasihar da ya yi wa jama'a, Sheikh Zakir Naik ya lissafa muhimman abubuwa da suka hada da salloli, neman daren Lailatul Qadri da sauransu
  • Hakan na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmi a Najeriya da kasashe dadaban daban suka shiga kwana na 4 a watan Ramadan a fadin duniya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Malamin addinin Musulunci na duniya, Dr Zakir Naik ya bukaci Musulmai su dage da ibada yayin da watan Ramadan ke cigaba da tafiya.

Baya ga lissafa abubuwa 25 da ya kamata a mayar da hankali game da su a Ramadan, Sheikh Zakir Naik ya gargadi mutane kan kame harshe a Ramadan.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya fadi dalilin shiga siyasa da neman gwamna a Gombe

Malamin Musulunci, Dr Zakir Naik
Dr Zakir Naik yana yi wa Musulmi nasiha. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Legit Hausa ta gano cewa malamin ya yi nasihar ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar 4 ga Ramadan 2026.

Kiran Zakir Naik kan abubuwa 25

Abubuwa 25 da Dr Zakir Naik ya bukaci Musulmi su yi a Ramadan sun hada da dagewa da salloli, yin sahur da sauransu. Ga jerin abubuwan a kasa:

1. Yin sallolin farilla guda biyar a cikin jam’i

2. Yin azumi a kowace rana ta Ramadan

3. Bayar da zakka idan ta wajaba a kan mutum

4. Nisantar dukkan abubuwan haram

5. Yin sallolin nafila, musamman kafin farillai da bayan su

6. Yin sahur

7. Jinkirta sahur zuwa kusa da asuba

8. Gaggauta buɗa baki

9. Cin dabino da shan ruwa yayin buɗa baki

10. Karanta addu’ar da ake yi bayan buɗa baki

11. Yin addu’a kafin buda baki

12. Ciyar da talakawa abinci

13. Yin sallar Tarawihi

Kara karanta wannan

Sheikh Bashir Aliyu ya yi wa Tinubu raddi kan rokon 'yan Najeriya su yafe masa

14. Yin sallar walaha (aƙalla raka’a 4)

15. Yin sadaka da kyauta da yawa

16. Karanta addu’o’i masu yawa da suka shafi ayyukan yau da kullum

17. Yawaita ambaton Allah SWT (yin zikiri)

18. Karanta Alƙur’ani gwargwadon iko tare da fahimtar ma’anarsa

19. Neman gafarar Allah

20. Yawaita aikata ayyukan alheri

21. Idan wani ya tsokane ka, kada ka yi martani, sai ka ce “Ina azumi”

22. Yin i’tikafi a kwanaki 10 na ƙarshen Ramadan

23. Neman daren Lailatul Qadir

24. Yin sallar dare, musamman a kwanaki 10 na ƙarshe

25. Tsarkake zuciya

Malamin ya kara da cewa yana da kyau Musulmi ya sani cewa azumi ba ya inganta sai an nisanci ƙarya, alfasha da sauransu.

Bola Tinubu zai ciyar da talakawa

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin ciyar da talakawa a watan Ramadan a fadin Najeriya.

Shugaban kasar ya nada Sarkin Kano na 15, mai martaba Aminu Ado Bayero shugabancin kwamitin domin lura da yadda zai yi aiki.

Kwamitin ya hada da malaman addinin Musulunci, ma'aikatan gwamnati da 'yan siyasa ciki har da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng