Gwamnati Ta Fitar da Albashin da Ake ba Tinubu, Shettima da Ƴan Majalisar Tarayya

Gwamnati Ta Fitar da Albashin da Ake ba Tinubu, Shettima da Ƴan Majalisar Tarayya

  • A Najeriya, shugabanni na karbar albashin da ya haura N3m a shekara, yayin da mafi karancin albashi na talakawa ya ke N70,000 a wata
  • Rahoton hukumar kula da albashi na 2007 ya nuna cewa shugaban kasa na karbar albashin N3.5m sannan yana samun alawus din N14m
  • Binciken Legit Hausa ya gano cewa, ministoci na karbar sama da Naira miliyan 7 a shekara, yayin da 'yan majalisa ke amfana da sama da N9m

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A Najeriya, kasar da kashi 75 na mutanen karkararta ke fama da talauci, na kashe miliyoyin Naira duk shekara wajen biyan manyan shugabanni albashi da alawus-alawus.

Rahoton albashi da alawus da hukumar kula da albashi da alawus ta kasa (RMAFC) ta fitar a 2007 ya bayyane irin makudan kudaden da ake ware wa shugabannin Najeriya.

Kara karanta wannan

Musa Kwankwaso ya faɗi maƙarƙashiyar da ake shiryawa NAHCON, Sheikh Pakistan

Hukumar RMAFC ta fitar da bayani game da albashin shugaban kasa, ministoci, da 'yan majalisar tarayya
Shugaba Bola Tinubu yayin da yake jawabi ga gamayyar 'yan majalisar tarayya a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Wannan rahoto ya shafi shekaru daga Fabrairu 2007 zuwa Yuni 2009, kuma har zuwa yau ba a fitar da wani cikakken sabon tsarin da ya maye gurbinsa a hukumance ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta zakulo bayanai daga wannan rahoto, inda ta duba takamaiman bayanan da suka shafi Shugaban Kasa, Mataimakin Shugaban Kasa, Ministoci, Sanatoci da ‘Yan Majalisar Wakilai.

Shugaban kasa: Mafi girman albashi

Shugaban kasar Najeriya yana karbar albashin shekara-shekara na Naira miliyan 3.5 (₦3,514,705). Amma wannan ba shine cikakken abin da yake samu ba.

Lamba daya na kasar yana karɓar albashi da alawus da jimillarsu ta haura ₦10m a kowacce shekara.

Wannan kudin ya haɗa da abubuwa kamar haka:

  • Albashi na Shekara − ₦3,514,705.00 a shekara
  • Alawus na wahalar aiki: ₦1,757,350.50 a shekara
  • Alawus din mazaba: ₦8,786,762.50 a shekara

Jimilla: ₦14,058,820.00

Sauran alawus:

  • Alawus na sallama bayan kammala wa’adin aiki: ₦10,544,115.00
  • Hutu: ₦351,470.50 sau daya a shekara
  • Bashin mota: − ₦14,058,820.00, za a biya kafin ƙarshen wa’adin aiki

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa ake barazanar rufe Facebook da Instagram a Najeriya

Shugaban kasa yana amfani da jirgi na musamman, yana da asibiti a fadar shugaban kasa, da kuma rundunar sojoji da ‘yan sanda da ke kula da tsaronsa da na iyalansa.

Mataimakin shugaban kasa: Albashin sama da N9m

Mataimakin shugaban kasa shima yana cikin masu jin daɗin wannan tsari. Yana karɓar albashi da alawus da suka kai ₦9,254,928.00 a kowacce shekara.

Ga yadda aka rarraba kudin:

  • Albashi na shekara: ₦3,031,572.00
  • Alawus din wahalar aiki: ₦1,515,786.00
  • Alawus na matsayi: ₦1,010,524.00
  • Alawus din mazaba: ₦1,515,786.00
  • Alawus na tafiye-tafiye: ₦1,181,260.00

Mataimakin shugaban kasa yana da motoci, dakunan aiki da taro, tsaro, da sauransu. Baya ga wannan, yana amfana da gidajen gwamnati da kayan aiki, wanda su ma kudinsu na da tsada matuka.

Ministoci: Mukarraban da ke karbar miliyoyi

Manyan ministoci da na cikin gida, su na karbar Naira miliyan 2.02 (₦2,026,400) a matsayin albashi na shekara.

Amma kowanne minista guda yana karɓar akalla ₦7,782,967.00 a shekara, na albashi da alawus kamar yadda rahoton ya nuna.

Ga yadda aka rarraba kudin:

  • Albashi na shekara: ₦2,026,400.00
  • Alawus na wahala: ₦1,015,320.00
  • Alawus na matsayi: ₦506,600.00
  • Alawus din mazaba: ₦1,519,980.00
  • Alawus na zama da sufuri: ₦1,290,667.00
  • Sauran alawus: Kamar haya da kayan aiki

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta dare gida 2, an samu hatsaniya kan Seyi Tinubu

Ministoci na amfana motoci da gidaje daga gwamnati, da damar yin amfani da ma’aikata da ofisoshi da aka tanada na musamman.

Baya ga haka, wasu alawus din ba sa cikin takardar albashin kai tsaye, kamar kudin tafiya kasashen waje da horar da ma’aikata.

'Yan majalisar dattawa: Albashin aiki da na mazaba

Kowacce jiha a Najeriya, na da sanatoci uku da ke wakiltarta a majalisar dattawa, kuma suna karbar albashin da ya haura ₦2m a shekara.

Amma abinda ya fi daukar hankali shine yawan alawus da ake biya musu:

What's the total?

  • Albashi na shekara: ₦2,026,400:00
  • Sanya mai da gyaran mota: ₦1,519,800.00 a shekara
  • Hadimi (PA): ₦506,600.00
  • Ma’aikatan cikin gida: ₦1,519,800.00
  • Kudin shakatawa da nishadi: ₦607,920.00 a shekara
  • Lantarki da sauran kayan amfani: ₦607,920.00 a shekara
  • Jaridu da Mujallu: ₦303,960.00 a shekara
  • Alawus na sutura: ₦506,600.00
  • Gyaran gida: ₦101,320.00 a shekara
  • Alawus na mazaba: ₦5,066,000.00
  • Kudin haya: ₦4,052,800.00
  • Kayan daki: ₦6,079,200.00
  • Alawus na yawon aiki: ₦37,000 kowace rana
  • Kuɗin tafiya kasashen waje: $950 a kowace rana
  • Hutu na lokaci-lokaci: ₦202,640.00 ana biya sau daya a shekara
  • Kudin sallama bayan kammala wa’adin aiki: ₦6,079,200.00 ana biyan shi bayan kammala wa’adin aiki
  • Bashin siyan mota: ₦8,105,600.00 ana bayarwa da sharadin a biya kafin wa’adin aiki ya cika

Kara karanta wannan

Sabon shugaban NNPCL ya ci gaba da fatattaka, ya kori shugabannin matatun mai 3

'Yan majalisar wakilai: Albashin aiki da na mazaba

Mambobin majalisar wakilai suna karbar albashin ₦1,985,212.50 a kowace shekara. A cewar rahoton, kowane ɗan majalisa yana karɓar sama da ₦7m na alawus.

Wannan ya haɗa da:

  • Shan mai da gyaran mota: ₦1,488,909.40 a shekara
  • Hadimi (PA): ₦496,303.12 a shekara
  • Ma’aikatan cikin gida: ₦1,488,909.40 a shekara
  • Nishadi: ₦595,563.75 a shekara
  • Lantarki da sauran kayan amfani: ₦595,563.75 a shekara
  • Sutura: ₦496,303.12 a shekara
  • Gyaran gida: ₦99,260.62 a shekara
  • Alawus din mazaba: ₦1,985,212.50 a shekara
  • Jaridu da mujallu: ₦297,781.90 a shekara
  • Kudin haya: ₦3,970,425.00 a shekara
  • Kayan daki: ₦5,955,637.50 a shekara
  • Alawus na yawon aiki: ₦35,000 kowace rana
  • Tafiye-tafiyen kasashen waje: $900 kowace rana
  • Hutu na lokaci lokaci: ₦198,521.25 sau daya a shekara
  • Alawus na sallama bayan kammala wa’adin aiki: ₦5,955,637.50
  • Bashin mota: ₦7,940,850.50, za a biya kafin ƙarshen wa’adin aiki
Albashin shugaban kasar Najeriya ya nuna na karamin ma'aikacin gwamnati sau 65
'Yan kwadago a ranar ma'aikata ta 2024 | Shugaban kasa, Bola Tinubu. Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT
Source: Facebook

Yadda albashinsu ke bambanta da na talaka

A lokacin da aka tsara wannan rahoton, ma’aikacin gwamnati mafi karancin albashi na karbar ₦18,000 a wata, wanda ke nufin ₦216,000 a shekara.

Kara karanta wannan

An dakatar da manyan alkalan Najeriya 3, za su rasa albashin wata 12

Wannan yana nufin shugaban kasa yana karbar kusan ninki 65 na albashin talaka a shekara, yayinda 'yan majalisa ke karbar fiye da ninki 70.

Wannan rahoto ya kara bude ido kan tsadar mulki da kuma bukatar sake fasalin tsarin albashi, domin tabbatar da daidaito da adalci a tsakanin masu mulki da talakawa.

An ji albashin shugaban kasar Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban ƙasar Amurka na karɓar albashi na $400,000 a shekara, kuma an ce albashin yana fitowa ne daga harajin 'yan ƙasa.

An ce Shugaba Donald Trump bai karɓi albashi ba a mulkinsa na farko, yana raba kudin ga ma’aikatu don tallafa wa aikin gwamnati.

Bayan sauka daga mulki, shugaban ƙasar Amurka zai ci gaba da samun $244,000 a shekara, da tsaro, lafiya da tafiye-tafiye na gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com