Cikakken Albashi Da Allawus Din Shugaban Najeriya, Mataimakinsa Da Na Gwamnoni Da Mataimakansu Ya Bayyana

Cikakken Albashi Da Allawus Din Shugaban Najeriya, Mataimakinsa Da Na Gwamnoni Da Mataimakansu Ya Bayyana

Batun albashin zababbun shugabanni a Najeriya lamari ne da ya dade yan Najeriya suna tafka muhawara a kansa.

Yayin da yan Najeriya ke ganin albashin da yan siyasan ke karba ya yi yawa, yan siyasan kuma a bangarensu su kan kare kansu ta hanyar bada dalilan da yasa suke karbar irin wannan albashin.

Buhari da Osinbajo
Albashi, Allawus Din Shugaban Najeriya, Mataimakinsa, Gwamnoni Da Mataimakansu, Takarda Daga RMAFC Ta Bayyana. Hoto: Femi Adesina.
Asali: Facebook

Daga cikin ayyukan hukumar tattara kudaden shiga da kasafin kudi akwai daidaita albashin da ya kamata masu rike da mukaman siyasa su samu ciki har da shugaban kasa, mataimakinsa, gwamnoni, mataimakansu, ministoci, kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, yan majalisa da sauran ma'aikatan gwamnati.

Wata takarda da aka wallafa a shafin intanet na RMAFC ya nuna albashi da allawus din shugaban kasa, mataimakinsa da wasu tun daga Fabrairun 2007 zuwa Yunin 2009.

Albashin shugaban kasa da allawus

Kara karanta wannan

2023: Ka Maye Gurbin Shettima Da Kirista, Matasan APC Suka Fada Wa Tinubu

A cewar takardar ta RMAFC, albashin shugaban kasa har da allawus na shekara guda shine N14,058,820:00 (N14.0m).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na nufin duk wata shugaban kasar na samun N1,171,568:20 (N1.17m).

Albashin Shugaban Kasa
Albashi, Allawus Din Shugaban Najeriya, Mataimakinsa, Gwamnoni Da Mataimakansu, Takarda Daga RMAFC Ta Bayyana. Hoto: rmafc.gov.ng.
Asali: UGC

Albashi da allawus din mataimakin shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasa na karbar 12,126,290:00 (N12.1m) duk shekara idan aka hada albashinsa da allawus.

A cewar takarda, duk wata mataimakin shugaban kasar na samun 1,010,524:16 (N1.01m).

Albashin mataimakin shugaban kasa.
Albashi, Allawus Din Shugaban Najeriya, Mataimakinsa, Gwamnoni Da Mataimakansu, Takarda Daga RMAFC Ta Bayyana. Hoto: Hoto: rmafc.gov.ng.
Asali: UGC

Albashi da allawus din gwamnoni

Takardar ta RMFAC ta nuna cewa gwamnonin Najeriya na samun N7,782,967:50 (N7.78m) a matsayin albashi da allawus duk shekara.

Abin da suke samu duk wata shine N648,580:62.

Albashin gwamnonin jiha
Albashi, Allawus Din Shugaban Najeriya, Mataimakinsa, Gwamnoni Da Mataimakansu, Takarda Daga RMAFC Ta Bayyana. Hoto: rmafc.gov.ng.
Asali: UGC

Albashi da allawus din mataimakin gwamna

Abin da mataimakin gwamna ya ke samu (albashi da allawus) a shekara shine N7,392,752:50 (N7.39m).

Kudin da kuma suke samu duk wata shine N616,062:69.

Kara karanta wannan

Zan gyara fannin ilimi cikin wata shida idan na gaji Buhari, inji wani dan takara

Albashin mataimakan gwamna
Albashi, Allawus Din Shugaban Najeriya, Mataimakinsa, Gwamnoni Da Mataimakansu, Takarda Daga RMAFC Ta Bayyana. Hoto: rmafc.gov.ng.
Asali: UGC

A Lura: Takardar ta RMFAC na Fabrairun 2007 zuwa Yunin 2009 ne. Don haka, akwai yiwuwar za a iya samun banbanci da albashi da allawus din shugaban kasa, mataimaikinsa, gwamnoni da mataimakansu na yanzu ko kuma ya zama daya.

Jerin Jihohin Najeriya 15 Da Ake Biyan Malaman Makaranta N30,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi

Shekaru uku bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar albashi mafi karanci, malaman frimare da sakandare na jihohi 15 da birnin tarayya Abuja kawai suke morar karin albashin da aka yi na N30,000.

Kungiyar malamai ta Najeriya, NUT ce ta bayyana hakan kamar yadda The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel