Allah ne ya bamu mulki amma talakawa ne suka zabe mu: Aisha Buhari ta sake yin 'gugar zana'

Allah ne ya bamu mulki amma talakawa ne suka zabe mu: Aisha Buhari ta sake yin 'gugar zana'

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba bakuwa ba ce wajen fito wa fili ta bayyana abinda ke ran ta dagane da al'amuran gwamnati da masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin mijinta.

A wannan karon Aisha Buhari wani faifan bidiyo na fitaccen malamin Islama da ke Kano, Sheikh Abdallah Gadon Kaya, tare da rubuta takaitaccen sakon gargadi a kan masu rike da mukami da su ke yin aiki da abinda suke fada.

Da yake koka wa a kan halin 'kuruciyar bera' a wurin shugabannin a Najeriya, a cikin faifan bidiyon, Sheikh Abdallah ya ce, "shugabanni na sace kudin kasa a lokacin da bama iya zuwa jami'o'i da asibitoci".

Da take yada faifan bidiyon a shafinta na dandalin sada zumunta (Instagram), Aisha ta rubuta gargadin cewa; "hattara ga masu rike da Mukamai! Wallahi Allah ya dora mu kan mulki da kuma kokarin malamai da talakawa! Don Allah mu bi shawararsu mu yi wa al'umma adalci! Subhanalla!

DUBA WANNAN: Sayen motocin biliyan N5.5: Wasu kungiyoyi uku da 'yan kishin kasa 6,716 sun shigar da karar majalisa

Sheikh Abdallah ya cigaba da cewa; "ina kira ga shugabanni masu satar kudin bayin Allah, su gina gidaje da kudin mutane, su tafi kasashen waje da kudin mutane. Akwai dabbanci da rashin hankali,"

"Kowa idan garin Allah ya waye fita yake ya nemi abin da zai ci amma shi kuma wani ya kwanta a kan dukiyarmu yana abin da ya ga dama da ita."

Kazalika, babban Malamin ya koka a kan yadda gwamnonin ke yin burus da batun yi wa jama'a aiki har sai an roke su.

Mutane kusan 200 ne suka mayar da mabanbantan ra'ayi tare da musayar yawu a kan faifan bidiyon da sakon da Aisha ta wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel