Gwamnati Ta Fadi Yadda Hadin Gwiwa da Saudiyya zai Warware Matsin Tattalin Arziki

Gwamnati Ta Fadi Yadda Hadin Gwiwa da Saudiyya zai Warware Matsin Tattalin Arziki

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai shirin da ake yi na samar da karin ayyukan yi ga matasan Najeriya
  • Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta himmatu wajen rage tsadar farashi
  • Edun na wannan bayani ne bayan ya dawo daga kasar Saudiyya inda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta himmatu wajen rage tsadar rayuwa ta hanyar rage farashin abinci nan da shekarar 2025.

Da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Lahadi a Legas, ya fadi hanyar da za a bi wajen cimma manufar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi wankin babban bargo ga gwamnan Bauchi kan haraji

Tinubu
Gwamnatin tarayya ta fadi shirin samar da ayyukan yi Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Mistan Wale Edun ya bayyana cewa akwai shirin da aka yi da gwamnatin Saudiyya da zai saukaka halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta shiga yarjejeniya da Saudiyya

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa za a samar da karin ayyukan yi a sabuwar shekara bayan wata ziyarar zuba jari da aka kai Saudiyya.

Edun na wannan bayani ne bayan ya dawo daga Saudiyya inda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya don kara karfafa shirye-shiryen zuba jari da Shugaba Bola Tinubu.

Najeriya na shirin inganta noma

Edun ya bayyana cewa Najeriya tana tsakiyar lokacin noman damina, kuma ana kokarin tabbatar da samun girbin damina mai albarka.

Ya bayyana cewa hakan zai rage farashin abinci, da rage hauhawar farashi da kuma tsadar rayuwa ga talakan Najeriya.

Kamfanin Saudiyya ya zuba jari a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce Kamfanin Saudi Agricultural Livestock Investment ya kara zuba jari da karin dala biliyan 1.2.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ziyarci Tinubu a Legas, an ji abin da suka tattauna a cikin bidiyo

Wale Edun ya ce;

“Wannan irin mu’amalar ce da Shugaban kasa ya dauki matakan daidaita yanayin tattalin arzikin Najeriya don karfafa irin wannan zuba jari da jawo sabbin hannayen jari.”

Ministan ya kara da cewa ana sa ran wannan zuba jari zai kara yawan kudaden shiga na kasashen waje, samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki.

Gwamnatin Tinubu zai taimaki magidanta

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta bayyana tsari da ta bijiro da shi domin taimaka wa magidanta, a wani shiri na inganta rayuwar talakawa.

Ministan jin kai da yaki da fatara, Nentawe Yilwatda ya ce gwamnatin Bola Tinubu za ta taimaki 'yan Najeriya Miliyan 75 inda za a raba tallafin N25,000 ga wasu daga cikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.