Gwamnatin Tinubu Ta Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta'addanci, Za Ta Dauki Mataki

Gwamnatin Tinubu Ta Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta'addanci, Za Ta Dauki Mataki

  • Gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta bankaɗo wasu mutum 15 da suka haɗa da ƴan canji mutum shida masu ɗaukar nauyin ta'addanci
  • An bayyana hakan ne a cikin wani saƙon imel, inda aka bayyana cewa mutanen suna karɓa ko tura kuɗi a madadin ƴan ta’addan
  • Ɗaya daga cikinsu shi ne Tukur Mamu, wanda a halin yanzu gwamnatin tarayya ke tuhuma kan zargin taimakawa ƴan ta’addan da suka kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Tinubu ta gano wasu mutum 15 da ake zargi da ɗaukar nauyin ta’addanci.

Daga cikin masu ɗaukar nauyin ta'addancin akwai mutum shida masu yin canjin kuɗi da wasu kamfanoni tara.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Shugaba Tinubu ya fadi lokacin da tsadar rayuwa za ta kare a Najeriya

Gwamnatin ta fadi masu daukar nauyin ta'addanci
Gwamnatin Tinubu ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce hakan ya bayyana ne a wani saƙon imel da hukumar NFIU ta aika mata a daren ranar Talata, 19 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki gwamnati za ta ɗauka?

Ta kuma ci gaba da cewa kwamitin NCS (mai sanya takunkumi) ya gana kan lamarin a ranar 18 ga watan Maris, 2024 inda ya bada shawarar sanya takunkumi kan mutanen da ake zargi da ɗaukar nauyin ta'addanci.

Daga cikin mutanen akwai Tukur Mamu, wanda a halin yanzu gwamnatin tarayya ke tuhuma a kotu bisa zarginsa da taimakon ƴan ta’addan da suka kai hari kan titin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja a watan Maris, 2022.

Takardar ta bayyana cewa Mamu ya ɗauki nauyin ta'addanci bayan ya karɓi kuɗin fansa $200,000 ga ƴan ta’addan ISWAP, domin sako waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan na Kaduna.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da ƴan takara 2 da ƙusoshin APC kan muhimmin batu a Villa, bayanai sun fito

Gwamnati ta gano maharan cocin Ondo

A cewar takardar, ɗaya daga cikin mutanen shi ne wanda ake zargin ya kai hari cocin St. Francis Catholic Church Owo, jihar Ondo a ranar 5 ga watan Yuni, 2022, da kuma gidan gyaran hali na Kuje, Abuja a ranar 5 ga watan Yuli, 2022.

An kuma bayyana wani da ke cikin takardar a matsayin ɗan ƙungiyar Ansarul Muslimina Fi Biladissudam, ƙungiyar ta’addanci da ke da alaƙa da Al-Qaeda a yankin Maghreb.

An bankado sanata mai taimakon ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumomin tsaro sun bankaɗo wani babban Sanata a Arewa mai ɗaukar nauyin ta'addanci.

Ana dai zargin sanatan da taimakon ƴan ta'addan da suka addabi yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa ta Yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel