Babban Labari: Gwamnatin Najeriya Ta Cafke Jami’an Manhajar Binance, an Samu Ƙarin Bayani

Babban Labari: Gwamnatin Najeriya Ta Cafke Jami’an Manhajar Binance, an Samu Ƙarin Bayani

  • Rahotanni suna nuni da cewa gwamnatin Najeriya ta cafke wasu jami'an kamfanin crypto na Binance bayan sun shigo kasar
  • Kafar ƴada labaran Birtaniya, Financial Times ta ruwaito cewa jami'an sun zo Najeriya ne don bin ba'asin dakatarwar da gwamnati ta yi masu
  • FT ta tattaro cewa an kwace fasfo din jami'an, amma har yanzu mahukunta a Najeriya ba su ce komai game da wannan rahoto ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

An tsare wasu manyan jami'ai biyu na kamfanin Binance a Najeriya, a cewar Financial Times (FT), wata kafar yada labaran kasuwanci da ke Birtaniya.

FT ta tattaro cewa jami'an kamfanin sun tashi zuwa Najeriya ne biyo bayan matakin da kasar ta dauka na dakatar da Binance daga aiki a kasar a makon jiya.

Kara karanta wannan

Hukumar NCC ta umurci MTN, Glo da sauransu da su toshe layukan da babu NIN, ta fadi rana

An kama jami'an Binance a Najeriya
Har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta yi magana akan kama jami'an na Binance ba. Hoto: @officialABAT, @binance
Asali: UGC

Har yanzu mahukunta ba su bayar da cikakken bayani kan dalilin tsare ma’aikatan na Binance ba, kuma babu tabbas kan ko an tuhume su da wasu laifukan da suka saba wa dokokin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta rufe amfani da manhajojin crypto

Premium Times ta ruwaito a makon jiya cewa gwamnatin tarayya ta toshe manhajar Binance da sauran kamfanonin crypto don daidaita farashin dala da kudin kasar.

Baya ga Binance, an toshe wasu manhajojin kamar Forextime, OctaFX, Crypto, FXTM, Coinbase, da Kraken, da sauransu.

Babban Bankin Najeriya (CBN) a ranar Talata ya nuna damuwa kan dala biliyan 26 da suka bi ta Binance Najeriya a cikin shekarar da ta gabata daga “kafofin da ba a tantance ba”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel