An Daure Mai Kamfanin Crypto Shekaru Dubu 11 A Gidan Kaso Kan Zargin Damfara A Turkiyya
- Wata a kotu a kasar Turkiyya ta daure mai kamfanin Thodex na Crypto tsawon shekaru dubu 11 a gidan kaso
- Ana zargin Faruk Fatih Ozer da kirkirar kamfanin Crypto da ke yashe kudaden jama'a da damfararsu
- Masu gabatar da kara na zargin Ozer ya tsere kasar Albaniya a 2021 da kudaden jama'a Dala miliyan 30 wadanda su ka zuba a kamfanin
Turkiyya - Kotu ta tasa keyar Faruk Fatih Ozer shekaru dubu 11,196 a gidan kaso kan zargin damfara a yanar gizo ta hanyar amfani da kudaden Crypto.
An daure Faruk wanda shi ne ya kirkiri Crypto da 'yan uwansa guda biyu kan damfara da kuma kirkirar kamfanin zalunci.
![Kotuda daure wani a gidan kaso kan zargin damfara a Turkiyya Kotuda daure wani a gidan kaso kan zargin damfara a Turkiyya](https://cdn.legit.ng/images/1120/d6ac7bfca00209c0.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
Meye ake zargin matashin a Turkiyya?
Masu gabatar da kara sun bukaci a yanke wa mamallakin kamfanin Thodex, Faruk Fatih daurin shekaru 40 a gidan kaso, cewar Euronews.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Anadolu News Agency ta tattaro cewa 'yan uwan nashi sun samu hukunci daya yayin da aka yanke hukuncin a ranar Alhamis 7 ga watan Satumba.
Faruk ya ce:
"Idan har zan kirkiri kamfanin da zai zalunci jama'a, ba zan yi shi cikin ganganci ba da rashin kwarewa."
Ana zargin Ozer ya gudu kasar Albaniya da Dala biliyan 2 na jama'a a 2021 wanda daga bisani aka karyata yawan kudaden.
Masu gabatar da kara sun zargi Ozer ya tura kudaden kimanin Dala miliyan 30 a wasu sirrantattun asusun bankuna.
Turkiyya ta yi kaurin suna wurin daure mutane a gidan kaso da shekaru masu yawa, cewar Vanguard.
Wannan na zuwa ne bayan kasar ta soke hukuncin kisa a shekarar 2004 don samun damar shiga Kungiyar Nahiyar Turai (EU).
Har ila yau, ana zargin 'yan uwan Ozer guda biyu da handame Dala miliyan 50 na kwastomomin kamfanin.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/83643e1198df54c9.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa
'Yan Crypto sun samu kudade bisa kuskure
A wani labarin, 'yan Crypto sun bayyana cewa sun samu kudade a asusun su bisa kuskure daga wani kamfani na Crypto.
Mafi yawan 'yan Crypto a Najeriya sun bayyana cewa sun wayi gari da biliyoyin kudade a asusun su.
Ana zargin wani kamfani ne ya yi kuskurem fasaha tare da tura kudaden a asusun mutane da ke ta'ammali da harkar Crypto.
Asali: Legit.ng