Kaduna: Sojoji Sun Yi Ajalin Kasurgumin Ɗan Bindiga, Bangaje da Wasu Hatsabibai 3

Kaduna: Sojoji Sun Yi Ajalin Kasurgumin Ɗan Bindiga, Bangaje da Wasu Hatsabibai 3

  • Wani kasurgumin ɗan bindiga ya gamu da ajalinsa bayan mummunan artabu da dakarun sojojin suka yi a jihar Kaduna
  • Yayin harin, sojojin sun hallaka 'yan bindiga hudu ciki har da hatsabibin ɗan ta'adda, Dogo Bangaje da wasu miyagu uku
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar ga manema labarai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Rundunar sojojin Nigeria ta hallaka 'yan bindiga hudu a wani farmaki a jihar Kaduna.

Dakarun 'Operation Whirl Punch da ke Arewa maso Yamma sun yi nasarar hallaka miyagu ciki har da kasurgumin ɗan bindiga, Dogo Bangaje.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama yan bindiga da matsafi da gashin mutum

Sojoji sun hallaka kasurguman 'yan bindiga 4 a Kaduna
Rundunar sojoji ta yi nasarar hallaka wasu hatsabiban 'yan bindiga 4 a Kaduna. Hoto: HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Yaushe aka hallaka 'yan bindiga a Kaduna?

Lamarin ya faru a karamar hukumar Giwa da ke jihar inda aka tafka mummunan fada wanda ya yi sanadin mutuwar 'yan bindigan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan tsaron cikin gida a jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook.

Kwamishinan ya ce an yi nasarar kisan miyagun ne a farmakin da dakarun suka kai a Tumburku da Sabon Sara.

Sojoji sun farmaki matsugunin 'yan bindiga

Aruwan ya ce dakarun sun kai farmakin bayan samun bayanan sirri inda suka hango miyagun suna kokarin sauya wuri zuwa Sabon Sara.

A wani hari makamancin wannan, dakarun sojoji sun farmaki kauyen Basurfe da ke Kudu maso Yammacin Kindandan.

Yayin harin, rundunar sojojin ta hallaka mayaka biyu tare da lalata matsuguninsu da suke ba 'yan uwansu kulawa.

Kara karanta wannan

Yayin da ake wahalar man fetur, Gwamna zai rufe gidajen mai da ke kara farashi

Har ila yau, dakarun sun yi nasarar kwato muggan makamai da kayan shaye-shaye da kuma magunguna.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa sojojin Najeriya masu yaƙi da ta'addanci a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma sun samu nasara kan ƴan ta'adda a ranar Talata.

Dakarun sojojin sun nuna bajinta inda suka daƙile yunƙurin ƴan ta'adda na yin garkuwa da mutane tare da ceto mutanen da aka yi yunƙurin sacewa.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta fitar a shafinta na manhajar X a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel