Taron Samar da Tsaro a Jihohin Arewa, Gwamnan Kano Ya Isa Kasar Amurka

Taron Samar da Tsaro a Jihohin Arewa, Gwamnan Kano Ya Isa Kasar Amurka

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya isa kasar Amurka domin halartar wani taron tattaunawa kan matsalar tsaro a Arewa
  • Taron na kwanaki uku zai samu halartar gwamnonin Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger, Sokoto, Kebbi, Jigawa, Plateau
  • Gwamna Abba ya bayyana cewa taron zai mayar da hankali wajen kawar da matsalolin da ke barazana ga rayuka da abinci a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya isa kasar Amurka domin halartar wani gagarumin taron tattaunawa kan tsaro da Cibiyar Zarin Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya isa kasar Amurka
Gwamna Abba Yusuf ya je Amurka ne domin halartar taro kan matsalar tsaro a Arewa. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Malam Sunusi Bature, babban daraktan yada labarai na Gwamnatin Abba ya fitar a ranar Laraba a Kano.

Kara karanta wannan

Abin da ba a taba yi ba: Dan Najeriya ya kafa tarihi a duniyar wasan 'Chess', Tinubu ya yaba masa

Taron na kwanaki uku zai samu halartar gwamnonin Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger, Sokoto, Kebbi, Jigawa, Plateau, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufofi na gudanar da taron Amurka

Bature ya ce taron zai magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya tare da samar da hanyoyin magance kalubalen daga tushe.

Ya ce taron zai baiwa gwamnonin damar zurfafa fahimtar illar rashin tsaro kan tattalin arziki da kuma hanyoyin tabbatar da samuwar zaman lafiya a Arewacin Najeriya.

Kwararru a cibiyar za su kuma fadada ilimin mahalarta taron game da dabarun dakile rikice-rikice a Arewa ta hanyoyin da ba a bukatar amfani da makamai.

Gwamna Kano ya isa kasar Amurka

Jim kadan bayan isarsa dakin taron, Gwamna Abba Yusuf ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) cewa:

Kara karanta wannan

29 ga Mayu: Abubuwan da gwamnati ta shirya yi a bikin cikar Tinubu shekara 1 a mulki

"Yanzu haka ina a Washington DC, tare da wasu gwamnonin Arewa domin halartar taron tsaro da zaman lafiya wanda Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya.
"Taron dai wani bangare ne na kudirin yankin na inganta hadin gwiwa tsakanin jihohinmu wajen kawar da matsalolin da ke barazana ga rayuka da abinci."

Kwamishina ya yi murabus a Ribas

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa kwamishinan shari'a na jihar Ribas, Farfesa Zacchacus Adangor ya yi murabus daga gwamnatin Similanayi Fubara.

Farfesa Adangor wanda dama dan a mutun ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya ajiye aikinsa a yau Laraba bayan da gwamnatin jihar ta canja masa ma'aikatar da yake jagoranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel