Za mu Hukunta Masu Boye Kaya, Shugaban Kasuwa Zai Yaki Tashin Farashin Abinci

Za mu Hukunta Masu Boye Kaya, Shugaban Kasuwa Zai Yaki Tashin Farashin Abinci

  • Yan kasuwar abinci ta kasa-da-kasa da ke garin Ibadan ta bayyana cewa za ta dauki mataki kabn duk dan kasuwar da ke boye abinci
  • Shugaban kasuwar, Alhaji Isma'ila Aderemi ne ya bayyana haka, inda ya ce sun dauki matakin rage farashin abinci domin samun sauki
  • Ya yi fariyar cewa babu wani dan kasuwar da ke boye kayan abinci, amma duk da haka ya gargadi wadanda ke da niyyar wannan aika-aika

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Oyo - Alhaji Ismaila Aderemi, Shugaban kasuwar kayan abinci ta kasa-kasa ta Bodija da ke Ibadan, jihar Oyo, ya gargadi ‘yan kasuwar da ke boye abinci da su shiga taitayinsu.

Kara karanta wannan

Farin ciki a jihar Arewa yayin da farashin shinkafa ya karye daga N60, 000

Shugaban 'yan kasuwar ya ce za su fara daukar mataki mai tsauri kan duk wanda aka kama yana boye kayan.

kasuwar kayan abinci
Kasuwar ta haramtawa masu sana'a a cikinta boye abinci Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

Ya ce sun zauna, tare da yanke shawarar rage farashin kayan abincin domin saukakawa al’umar yankin, kamar yadda Leadership news ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

“’Yan kasuwarmu na sayar da kayansu a kan farashin da ba a samu a wasu kasuwannin da ke ciki da wajen Ibadan.”
“Yan kasuwar sun dauki matakin ne saboda koke-koken jama’a kan matsin rayuwa da ake fuskanta a kasar nan na tashin farashi,” in ji Ismaila Aderemi.

Za a zakulo masu boye kaya a kasuwa

Da ya ke karin bayani kan matakin da za su dauka kan wadanda ke boye kayan abinci a kasuwar, Ismaila Aderemi, ya ce za su zakulo masu boye kaya ko kara farashi ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Tashin farashin Dala: Kokarin da CBN yake yi na daidaita Naira a kasuwar canji

Kuma a cewarsa, za su fuskanci hukunci daidai dokokin kasuwar.

Ya bayar da tabbacin cewa zuwa yanzu babu wani dan kasuwar da ke boye kaya domin daga farashi, kamar yadda peoples gazatte ya wallafa.

“Ina tabbatar maka zuwa yanzu ban samu wani dan kasuwa da boye kaya ba. Babu nu cikin boye kaya. Za ka iya zagayawa domin ka tabbatar.”

Shugaban kasuwar ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakin tabbatar da saukar farashin kaya a kasar nan.

Kamfanin Dangote ya musanta janyo tsadar kaya

Mun kawo mu ku labari cewa babbar darakta a kamfanin Dangote, Hajiya Fatima Dangote ta musanta cewa suna da hannu cikin kara tsadar abincin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Ta ce ko kamfanin Olam da ake zargi da dake sarrafa kayan abinci irinsu fulawa da sauran kayan abinci a yanzu ba ya karkashin kamfanin Dangote.

Asali: Legit.ng

Online view pixel