Dizal Zai Iya Karyewa Zuwa N700/L, Dillalan Mai Sun Yabawa Dangote Kan Karya Farashi

Dizal Zai Iya Karyewa Zuwa N700/L, Dillalan Mai Sun Yabawa Dangote Kan Karya Farashi

  • A yayin da 'yan Najeriya ke cuku-cukun sayen man dizal duk da tsadar da ya yi, dillalan mai sun yi wani albishir da ya yi wa 'yan kasa dadi
  • Kungiyar dillalan karkashin IPMAN ta ce tana sa ran cewa nan ba da jimawa ba farashin dizal zai kara karyewa zuwa N700 kan kowacce lita
  • IPMAN ta yi wannan ablishir din ne yayin da take jinjinawa matatar kamfanin Dangote na sauko da farashin dizal zuwa N1,000 daga N1,2000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya ta ce tana sa ran cewa matatar man Dangote za ta kara rage farashin dizal din ta zuwa Naira 700 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

Tashin farashin Dala: Kokarin da CBN yake yi na daidaita Naira a kasuwar canji

Dillalan mai sun fadi farashin da dizal zai iya kai wa nan gaba kadan
Dillalan sun alakanta karyewar dizal da karfin Naira da kuma sarrafa shi a matatar Dangote. Hoto: Dangote Group
Asali: Getty Images

Dizal: Dillalai sun yabawa matatar Dangote

Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Hammed Fashola ne ya bayyana haka a ranar Laraba, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fashola ya kuma yabawa matatar man Dangote bisa rage farashin man dizal daga sama da Naira 1,200 zuwa N1,000 a kan kowace lita.

Fashola, a zantawarsa da manema labarai, ya ci gaba da cewa ’yan kasuwar na da yakinin cewa har yanzu akwai yiwuwar farashin man dizal zai ragu.

Karyewar Dala ya shafi farashin dizal?

A cewarsa, karfin da Naira ta samu a kan Dalar Amurka da ma sauran kudade zai taimaka wajen kawo babban ragi a farashin da ake sayar da man dizal.

“Wannan ci gaba ne mai kyau, abin farin ciki ne. Abin da muka sa rai dama ke nan, kuma har yanzu muna da yakinin cewa dizal zai ƙara saukowa.

Kara karanta wannan

Dangote ya fadi dalilin zaftare farashin man dizal zuwa N1,000

"Domin idan aka kalli yadda farashin Dala yake a kan Naira a yanzu, kudin mu ya yi daraja sosai. Muna kuma sa ran Dalar za ta kara karyewa zuwa kasa da N1,000."

- A cewar Fashola.

"Dizal zai karye zuwa N700" - Dillalai

Mataimakin shugaban ya bayyana farashin zai kara karyewa ne saboda an kawar da kalubalen jigilar kaya, harajin kwastam tunda yanzu ana samar da kayan a cikin gida.

"Don haka, mu ’yan kasuwa, muna sa ran man diesel zai karye zuwa kamar Naira 700 a kan kowace lita; wannan ita ce addu’armu kuma a wannan matakin zai zama alheri ga kowa."
“Dukkanmu muna goyon bayan Dangote. Mun yaba kan yadda farashin yake saukowa, kuma har yanzu muna sa ran cewa farashin zai kara yin araha ga 'yan kasa."

- In jin mataimakin shugaban na IPMAN.

Har yanzu dizal yana nan a N1,500

Sai dai kuma rahoton jaridar The Cable ya nuna cewa har yanzu ana siyar da man dizal a kan N1,500 a gidajen mai dake Legas da Abuja a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Ana harin fetur ya koma N500, ‘yan kasuwa sun ci buri da matatun Fatakwal da Dangote

Farashin na nan a yadda yake duk da cewa matatar man Dangote ta sanar da rage farashin man ga ‘yan kasuwa daga N1,200 zuwa N1,000 a ranar 16 ga Afrilu.

Matatar Dangote ta karya farashin dizal

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto yadda matatar Dangote ta sanar da rage farashin dizal din daga N1,200 zuwa N1,000 a wajen 'yan kasuwa.

Ragin da aka sanar a ranar 16 ga Afrilu ya shafi 'yan kasuwar da ke dillancin mai daga matatar ne, wanda aka yi tunanin zai karya farashin a gidajen mai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel