'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Kusan Mutum 50 a Garuruwa 3 a Jihar Katsina

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Kusan Mutum 50 a Garuruwa 3 a Jihar Katsina

  • Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane a kauyukan kananan hukumomin Batsari da Malumfashi a jihar Katsina
  • Rahotanni sun nuna cewa kusan mutum 50 ciki har da mata da ƙananan yara ƴan bindigar suka sace a kauyuka 3 cikin wannan makon
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Katsina, Abubakar Sadiq, bai ɗaga waya ba yayin da aka tuntuɓe shi kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da akalla mutane 28 a kauyen Zamfarawar Madogara da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.

Wata majiya ce ta tabbatar da sace mutanen ga jaridar Daily Trust ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta, sun kashe bayin Allah sama da 20 a Kaduna

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
'Yan bindiga sun kai sabbin hare-hare a makon nan a jihar Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Twitter

Majiyar ta kuma bayyana cewa ƴan bindigan sun sace gomman mutanen ne ranar Alhamis ɗin da ta gabata da daddare lokacin da suka kai farmaki kauyen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙaramar hukumar Batsari na ɗaya daga cikin waɗanda ƴan ta'adda ke yawan kai hare-hare a jihar Katsina kusan sheƙaru 10 kenan.

Haka nan kuma a wani ɓangaren, ƴan bindiga sun kai sabon hari a Naduai duk a yankin Batsari inda suka yi garkuwa da mutane tare da cinna wa tulin tulin fulawa wuta.

Ƴan bindiga sun kai wani harin

A wani harin na daban kuma akalla mutane 20 galibi mata da ƙananan yara ƴan bindiga suka sace daga kauyen Na-Alma'da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a Katsina.

An tattaro cewa ƴan bindiga sun kutsa cikin kauyen a kan babura ranar Talata da ta gabata, suka aikata wannan ɗanyen aikin.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindinga sun kashe 'yan banga 3 tare da sace mutane masu yawa a wani sabon hari

Wani mazaunin garin wanda ya sha da kyar daga sharrin maharan, ya ce ‘yan bindigar sun kuma shiga gidaje tare da kwashe wasu kayayyaki masu daraja.

Mutumin ya ce:

"Sun yi garkuwa da 'yan mata, mata takwas masu shayarwa da jariransu, da mata biyu masu ciki."
"Sun kuma yi garkuwa da wani mutum da suka yanke masa hannu da kafarsa a kwanakin baya.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, bai ce komai ba kan lamarin har ya zuwa lokacin muka haɗa wannan rahoton.

Yan bindiga sun kashe mutum 23

A wano rahoton mun kawo masu cewa Ƴan bindiga sun kashe mutane akalla 23 yayin da suka kai sabon farmaki a kauyen Anguwar Danko da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a Kaduna.

Wani shugaban al'umma ya bayyana yadda ƴan bindigan suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi ranar Laraba da daddare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel