Mutane Sun Mutu da Rikici Ya Kaure Tsakanin Hausawa da Fulani a Arewacin Najeriya

Mutane Sun Mutu da Rikici Ya Kaure Tsakanin Hausawa da Fulani a Arewacin Najeriya

  • Akalla mutane hudu ne suka mutu yayin da rikici ya kaure tsakanin Hausawa da Fulani makiyaya a Gudu, jihar Sokoto
  • Shugaban ƙaramar hukumar Gudu, Alhaji Ummar Maikano ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu ana zaman sulhu
  • Sai dai har yanzu ba a iya gano abin da ya jawo rikicin ba, amma Maikano ya ce fadan ba zai rasa nasaba da saɓani a kan gona ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gudu, jihar Sokoto - Rikicin da ya barke tsakanin Hausawa da Fulani a karamar hukumar Gudu ta jihar Sokoto, ya yi sanadin mutuwar mutane hudu.

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da ya jawo fadan Fulani da Hausawa a jihar
Adadin mutanen da suka mutu a fadan Fulani da Hausawa a jihar Sokoto ya kai 4. Hoto: @Ahmedaliyuskt
Asali: Twitter

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Ummar Maikano wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Leadership ya ce fadan ya faru ne a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Gumi ya taka rawa wurin kubutar da dalibai 137 a Kaduna? Uba Sani ya fayyace gaskiya

Makiyayi ya fadi dalilin rikicin Hausawa-Fulani

Sai dai har yanzu ‘yan sanda ba su bayar da wani bayani ba kan lamarin da aka ce ya faru a Jimjimi, kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani makiyayi da ya zanta da jaridar ya ce:

“A ranar Larabar da ta gabata ne Hausawa suka dawo daga daji inda suka tarar da cewa wasu ‘yan uwansu biyu sun bata, shi ne suka yi zargin Fulani ne suka dauke mutanen.
“Duba da halin da ake ciki, shugabanmu ya umarce mu da mu bar matsugunanmu. Amma kafin mu kai ga yin hakan har Hausawan sun iso, suka kona rugagenmu, tare da kashe mana mutum biyu."

"Rikicin gona ne ya hada fadan" - Maikano

Amma, Sahara Repoters ta ruwaito cewar shugaban karamar hukumar ya ce fadan ya samo asali ne daga rikicin gona tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa manoma.

Kara karanta wannan

Ana alhinin mutuwar dalibai a Nasarawa, mata 4 sun mutu yayin karbar zakka a Bauchi

"A lokacin da wutar rikicin ta tashi, Hausawa sun je rugagen Fulani, amma basu tarar da kowa ba, sai dai, sun faɗa komar makiyayan."
"Lokacin da ƙura ta lafa, Fulani sun yi wa Hausawa ɓarna, amma an tabbatar da mutuwar mutane hudu, biyu daga kowanne ɓangare."

- A cewar Maikano.

Yan sanda ba su ce komai ba

Ko da aka tuntubi kakakin rundunar ƴan sanda na jihar Sokoto, ASP Rufa'i Ahmad, ya ce ba zai iya ba da tabbaci kan labarin ba.

Ahmad ya yi ikirarin cewa ba ya cikin garin yanzu amma zai fitar da rahoto da zarar ya samu cikakken bayani.

Sai dai shugaban karamar hukumar ya ce yanzu haka dai ana kan yin zaman sulhu da bangarorin biyu domin wanzar da zaman lafiya.

Fadan Fulani da Hausawa a Gwadabawa

Ba wannan ne karo na farko da Hausawa da Fulani ke karawa da juna a Sokoto ba, ko a watan Afrilu, Legit Hausa ta ruwaito cewa hakan ta taɓa faruwa a Gwadabawa.

An yi asarar rayuka da dama a wancan faɗan, wanda har ya rutsa da wasu jami'an tsaro da suka je kwantar da tarzoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel