Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Bayin Allah a Jihar Sakkwato

Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Bayin Allah a Jihar Sakkwato

  • Sojoji sun kashe wani ɗan bindiga mai hatsari da ke sanya kakin ƴan sanda yana yaudarar mutane a jihar Sakkwato
  • Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasa, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin sun samu wannan nasara ne ranar Laraba
  • Ya ce bayan wannan, sojoji sun halaka wani ɗan ta'adda a jihar Taraba tare da ƙwato nuggan makamai daga hannunsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Dakarun rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar halaka hatsabibin ɗan bindiga mai haɗari wanda ke shigar ƴan sanda yana aikata ta'addanci a jihar Sakkwato.

Sojojin sun kuma lalata ma'ajiyar magungunan ƴan bindiga da wuraren kiwon lafiyarsu a wani samame da suka kai ranar Laraba 20 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar gwamnati a watan azumi, sun tafka ɓarna a jihar Katsina

Sojojin Najeriya.
Sojoji sun samu nasara a Sokoto da Taraba Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasa, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa a X a ranar Alhamis (yau), 21 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Nwachukwu, dan ta’addan ya sha yin shiga a matsayin ɗan sanda wajen yaudara da yin garkuwa da mutane masu yawa da ba a san adadinsu ba.

Sojoji sun kashe wani a Taraba

Sanarwar wadda rundunar soji ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis ta ƙara da cewa:

"A wani samamen na daban da dakarun sojoji suka kai a jihar Taraba, sun yi nasarar kashe wani ɗan ta'adda a ƙauyen Kutoko da ke ƙaramar hukumar Takum a jihar."
"Baya ga haka, a samamen sojoji sun kuma kwato bindiga ƙirar AK-47 da Magazine ɗauke da alburusai huɗu na musamman masu nauyun 7.62mm."

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Daga karshe an fadi dalilin da ya sa aka kashe jami'an tsaron

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa irin wannan hare-hare da sojoji ke kai wa na ƙara tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya ta shirya kakkaɓe duk wani nau'i na ta'addanci.

A cewarsa, wannan wani ɓangare ne na yunƙurin rundunar soji wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali sun samu gindin zama a tsakanin al'umma.

Sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta ayyana Tukur Mamu, ɗan jarida a Kaduna da wasu mutum 14 a matsayin masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Legit Hausa ta tattaro muku sunayen mutanen da gwamnati ke zargi suna angiza wa ƴan ta'adda kuɗaɗe, wanda ya ƙunshi kamfanoni da ƴan canji 6.

Asali: Legit.ng

Online view pixel