Ana Shirin Gurfana Gaban Kotu, Ganduje Ya Aika Sako Zuwa Ga Gwamnatin Kano

Ana Shirin Gurfana Gaban Kotu, Ganduje Ya Aika Sako Zuwa Ga Gwamnatin Kano

  • Abdullahi Umar Ganduje ya bugi kirji da cewa shi yanzu ya zama turmi sha daka kuma bishiyar kuka da babu mai iya jijjiga shi
  • Ya yi wannan furucin ne yayin da kuma yake jaddadawa gwamnatin Kano cewa har yanzu dai shi ne shugaban jami'iyyar APC na kasa
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da ake shirin gurfanar da Ganduje a gaban babbar kotun Kano a yau Laraba kan tuhume-tuhumen rashawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A yayin da kowa ya zuba idanu ya ga yadda za a gurfanar da shugaban jam'iyyar APC na kasa a gaban kotu, Abdullahi Ganduje ya aika sako ga gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Babban lauya ya fadi abin da zai iya faruwa a shari'ar Ganduje

Ganduje ya aika muhimmin sako ga gwamnatin Kano
Ganduje ya shaidawa gwamnatin Kano cewa babu mai iya jijjige shi daga kujerar shugaban APC. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Ganduje ya shaidawa Gwamna Abba Yusuf cewa shi yanzu ya zama turmi sha daka kuma bishiyar kuka da babu mai iya jijjiga shi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan furucin ne yayin da kuma yake jaddadawa gwamnatin Kano cewa har yanzu dai shi ne shugaban jami'iyya mai mulki ta kasa, watau APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu mai iya jijjiga ni" - Sakon Ganduje

A cikin wani faifan bidiyo, an ga Ganduje a cikin dimbin magoya bayan jam’iyyar suna nuna mubayi'a ga Ganduje, inda aka ji yana cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya tabbatar da matsayinsa na shugaban jam’iyyar.

Ganduje ya ce:

“A jiya (Talata) na gana da shugaban kasa na yi masa bayani kuma ya ce kar in wani damu kai na. Kujerar da ake magana a kanta tawa ce, babu mai iya jijjige ni daga kanta.

Kara karanta wannan

Lauya a Kano ya fadi abin da ya kamata Ganduje ya yi, ya magantu kan zargin Gwamnati

“Ku gaya wa Gwamnatin Jihar Kano cewa kujerar shugaban jam’iyyar APC ta kasa a Najeriya ta na hannun Abdullahi Umar Ganduje. Kuma muna nan daram-dam."

APC na zargin gwamnatin Kano

Channels TV ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne jam’iyyar APC ta zargi gwamnatin jihar Kano da daukar nauyin wasu a gundumar Ganduje domin sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa.

Sai dai kuma gwamnatin ta yi gaggawar musanta hannu a cikin lamarin, inda ta yi ikirarin cewa lamarin "rikicin cikin gida ne kawai" a cikin jam'iyyar APC.

Ganduje zai gurfana gaban kotu?

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto wani matashin lauya a jihar Kano, Abba Hikima ya ce ba lallai bane Abdullahi Ganduje ya gurfana gaban kotu kamar yadda ake tunani.

Hikima ya ce Ganduje na iya amfani da wasu dabaru na shari'a wajen kare kansa daga shammaci, kamu ko kuma gurfana gaban kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel