Kotu Ta Dauki Mataki Kan Dakatarwar da Aka Yi Wa Ganduje Daga Jam'iyyar APC

Kotu Ta Dauki Mataki Kan Dakatarwar da Aka Yi Wa Ganduje Daga Jam'iyyar APC

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu matsala bayan kotu ta bayyana matsayarta kan dakatarwar da aka yi masa
  • Babbar kotun mai zamanta a jihar Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje daga jam'iyyar mai mulki a Najeriya
  • Kotun ta kuma hana shi bayyana kansa a matsayin mamba na jam'iyyar tare da jagorantar ayyukan kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata babbar kotu a jihar Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Kotun ta kuma bada umurnin hana Ganduje bayyana kansa a matsayin mamba na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Shugabannin APC za su sanya labule da Ganduje a Abuja, bayanai sun fito

Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje
Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga APC Hoto: @officialAPCNg
Asali: Twitter

Alƙalin kotun, mai shari'a Usman Malam Na'abba, shi ne ya bada umurnin a ranar Talata, 16 ga watan Afirilun 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa suka kai Ganduje ƙara a APC?

Umurnin na zuwa ne biyo bayan ƙarar da Halliru Gwanzo da Laminu Sani suka shigar ta hannun lauyansu Ibrahim Sa'ad, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Masu shigar da ƙarar waɗanda suka bayyana kansu a matsayin shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, sun bayyana cewa sun shigar da ƙarar ne a madadin shugabannin jam'iyyar na mazaɓar.

Halliru Gwanzo, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a na mazaɓar, shi ne ya sanar da dakatar da Ganduje, kwanaki biyu da suka wuce.

Hakazalika, kotun ta yi umurnin cewa daga yanzu Ganduje ya daina jagorantar dukkanin al'amuran kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

APC ta yi fatali da batun dakatar da Ganduje, ta dauki mataki kan masu hannu a ciki

APC ta yi fatali da dakatar da Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ƙasa ta yi watsi da dakatarwar da wasu shugabannin jam'iyyar a matakinazaɓa suka yi wa Abdullahi Umar Ganduje.

Jam'iyyar ta bayyana su a matsayin sojojin gona tare da shigar da ƙara a gaban babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egɓetokun, domin ya gudanar da bincike a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel