NNPP Ta yi Watsi da Zargin sa Hannu Wajen Dakatar da Ganduje Daga APC

NNPP Ta yi Watsi da Zargin sa Hannu Wajen Dakatar da Ganduje Daga APC

  • Jam'iyyar APC ta zargi NNPP a Kano da hannu wajen ingiza wasu 'yan jam'iyyar su kore shugabansu, Abdullahi Umar Ganduje
  • NNPP ta musanta zargin inda ta ce APC ba warware matsalarta na cikin gida ba tare da dora musu laifin da ba su ji ba ba su gani ba
  • Uwar jam'iyyar APC a Kano ta soke korar da mazabar Ganduje ta yiwa shugaban APCn tare da daukar matakin ladabtarwa kan wadanda suka ayyana korar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta nesanta kanta da rikicin cikin gida a jam'iyyar APC da har ta kai ga dakatar da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Ganduje: APC da PDP sun rikice, shugabanninsu sun shiga garari, an gano dalili

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya shaidawa manema labarai cewa ba su da alaƙa ta kusa ko nesa da duk wani abu da ke faruwa a APC.

Gwamnatin Kano ta musanta hannu cikin rikicin jam'iyyar APC
NNPP ta ce ba ruwanta cikin rikicin APC Hoto: UGC
Asali: UGC

A rahoton Daily Trust, Sunusi Bature ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu dake NNPP ba mu da alaƙa da duk wani abu da ke faruwa a cikin APC. Saboda haka wannan matsalarsu ce ta cikin gida, kuma kamata yayi su warware shi ba tare da ɗora laifin kan kowa ba."
"Matsalar da APC ke fuskanta shi ne ba su san doka ba. Wasu lokutan ba sa iya bambance tsakanin matsalar cikin gida da ta waje."

An zargi NNPP da hannu a korar Ganduje

A yammacin Litinin ne APC reshen jihar Kano ta yi zargin NNPP da hannu cikin dakatar da mazabar Ganduje ta yi masa.

Kara karanta wannan

Mambobin NNPP sun buƙaci Gwamna Yusuf na Kano ya yi murabus cikin sa'o'i 48, ta faɗi dalili

Haladu Gwanjo, mashawarcin jam'iyyar a bangaren sharia a Dawakin Tofa ne ya sanar da dakatar da shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

Suna zargin Ganduje da sama da fadi da kudin al'umma da ma sauran zarge-zargen cin hanci da rashawa.

An ladabtar da wadanda suka kori Ganduje

Awanni kaɗan bayan sanarwar dakatar da Ganduje daga jam'iyyar APC ne uwar jam'iyyar ta jiha ta dakatar da wadanda suka jagoranci sanar da dakatarwar.

Shugaban jam'iyyar a Kano, Abdullahi Abbas ya ce an dakatar da shugabannin har na tsawon watanni shida, inda ya ce suna sane da yadda wadanda suka bayyana dakatar da Ganduje ke tattaunawa da 'yan adawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel