Wahala Ta Kai Maƙura Bayan Jami'an Tsaro Sun Bindige Matashi Yayin Bin Layin Shan Mai

Wahala Ta Kai Maƙura Bayan Jami'an Tsaro Sun Bindige Matashi Yayin Bin Layin Shan Mai

  • Wahalar mai a jihar Legas ya yi ajalin wani matashi bayan sojoji sun bindige shi yayin bin layin siyan man fetur
  • Matashin mai suna Toheeb Eniasa ya gamu da tsautsayin a gidan man NNPCL da ke Ikoyi a jihar a jiya Laraba 1 ga watan Mayu
  • Lamarin ya faru ne bayan matashin ya dage sai jami'an sun bi layi kamar kowa yayin da suka zo shan mai a wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - An shiga fargaba bayan bindige wani matashi a jihar Legas a turereniyar bin layi a gidan mai.

Matashin mai suna Toheeb Eniasa ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya je siyan mai a gidan mai na NNPCL da ke Ikoyi a jihar.

Kara karanta wannan

Fadan daba: fusatattun matasa sun cinnawa kasuwa wuta a Lagos

Sojoji sun bindige matashi a gidan mai yayin bin layi
An shiga jimami bayan sojoji sun bindige wani matashi a Legas. Hoto: Benjamin Hundeyin.
Asali: Facebook

Yaushe aka bindige matashi a Legas?

Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Laraba 1 ga watan Mayu wanda ya jefa mutanen yankin a fargaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta tattaro cewa lamarin ya faru ne bayan wasu jami'an tsaro ne suka shigo gidan man domin shan mai a gaban jama'a.

Lamarin da ya jawo mutane suka ki amincewa da hakan ganin yadda suka dade a layi fiye da awanni, cewar Vanguard.

Shaidun gani da ido sun tabbatar cewa Eniasa ne yafi zaƙewa kan sai jami'an tsaron sai sun bi layi kamar kowa.

Hakan ne ya fusata daya daga cikinsu inda ya harbe shi tare da tserewa daga wurin nan take.

Mene mutane ke cewa kan lamarin?

Wani shaidar gani da ido da ake kira Ayo ya ce:

"Na gansu, wasu jami'an DSS ne suka zo siyan man amma sai suka ki bin layi wanda daman haka suka saba yi."

Kara karanta wannan

"Sako ga masarautar Zamfara": 'Yan bindiga sun saki bidiyon hadimin sarki da suka sace

"Layin Eniasa bai iso ba kuma ya ce musu ya kamata su bi layi ko su yi magana mai dadi a barsu su shiga."
"Daya daga cikinsu bashi da hakuri inda ya mari matashin wanda shi kuma ya faffaɗa masa magana kafin kace wani abu ya harbe shi."

Matasa sun cinnawa kasuwa wuta a Legas

A wani labarin, kun ji cewa 'Yan daba sun yi arangama a wata kasuwa da ke jihar Lagos, wanda ya kai ga raunata mutane da dama, sai dai har yanzu babu tabbacin asarar rai.

'Yab dabar sun kona shaguna da dama yankin Ile-Epo na jihar ta Lagos tare da yi wa juna raunuka bayan sun kwana suna hayaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel