Takaddamar El-Rufai da Uba Sani: Jam'iyyar APC Ta Fadi Wanda Take Goyon Baya

Takaddamar El-Rufai da Uba Sani: Jam'iyyar APC Ta Fadi Wanda Take Goyon Baya

  • Jam'iyyar APC ta nuna goyon bayanta ga gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani bisa ƙoƙarin da yake yi a jihar
  • Kakakin jam'iyyar wanda ya bayyana hakan ya ce jam'iyyar ta yaba da ayyukan ci gaban al'umma da gwamnan ke yi
  • Haka kuma jam'iyyar ta tabbatar da dakatarwar da ta yi wa shugabar mata saboda kalaman da ta yi a kan gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jam’iyyar APC a Kaduna ta yabawa Gwamna Uba Sani, kan faɗin adadin basussukan da ake bin jihar

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Salisu Wusono, kakakin jam’iyyar APC a Kaduna, ya yaba da matakan da gwamnan ya ɗauka na rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙin da ake fuskanta a jihar, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Sokoto ta ciyo bashin makudan kudi? Gwamna Ahmed ya fayyace gaskiya

APC ya goyi bayan Uba Sani
Jam'iyyar APC ta yabawa Gwamna Uba Sani Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Wusono ya kuma ce dakatarwar da aka yi wa Maryam Suleiman, shugabar mata ta jam’iyyar APC a jihar, za ta kasance har sai abin da hali ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dakatar da shugaban matan ta jam’iyyar APC ne bayan ta caccaki gwamnan bisa kalaman da ya yi kan basussukan da ya gada daga gwamnatin tsohon gwamnan jihar Nasir el-Rufai.

Waɗanne ayyuka Uba Sani ya yi?

A kalamansa:

"Waɗannan ayyukan sun haɗa da bada tallafi ga masu ƙananan sana'o'i 7,500, tallafi ga manoma 5,000, bayar da tallafin kuɗi da rarraba abinci ga marasa ƙarfi.
"Nasarar ceto ɗaliban makarantar Kuriga da jaddada ƙudirin gwamnatin na inganta tsaro a jihar Kaduna."

Meyasa APC ta dakatar da Maryam Suleiman?

Salisu Wusono ya tabbatar da cewa an dakatar da shugabar matan ne saboda abin da ta yi ya saɓawa kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Daga karshe Wike ya bayyana inda aka kwana kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Dakatarwar wacce a cewarsa ta har sai abin da hali ya yi ce, ta shafi muƙaminta da kuma zamanta mamba a jam'iyyar APC, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Kakakin na APC ya bayyana cewa ya kamata gwamnan ya mayar da hankali kada ya bari wasu masu ƙananan maganganu su hana shi gudanar da aikinsa.

'Ban yi nadama ba' - Maryam

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakatacciyar shugabar mata ta jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Maryam Suleiman, ta ce ba ta yi nadamar sukar da ta yi wa Gwamna Uba Sani ba.

Maryam ta bayyana cewa abin da gwamnan ya yi wa Nasir El-Rufai ƙarara cin amana ne duba da ɗawainiyar da ya yi da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel