Badakalar N855m: Kotu Ta Sami Ma’aikatan Banki da Laifin Sata, Ta Yanke Masu Hukunci

Badakalar N855m: Kotu Ta Sami Ma’aikatan Banki da Laifin Sata, Ta Yanke Masu Hukunci

  • Kotun Daukaka Kara ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar ga wasu ma'aikatan bankin Keystone guda biyu da wani dan Indiya
  • Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan samun mutanen da aikata laifuffuka 7 da suka shafi satar N855m da kuma zamba cikin aminci
  • Wannan hukuncin na kotun, ya zama tabbaci ne kan hukuncin da babbar kotun Legas ta fara yanke wa mutanen tun a shekarar 2019

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Kotun Daukaka Kara da ke Legas, ta yanke wa wasu ma'aikatan bankin Kyestone biyu hukuncin shekaru biyar a gidan yari.

Kotun Daukaka Kara ta yanke hukunci kan wasu ma'aikatan bankin Keystone
Kotun Daukaka Kara ta sami ma'aikatan banki da laifin satar N855m. Kotu: GettyImages
Asali: UGC

Kotu ta yanke wa ma'aikatan hukunci

Wannan hukuncin, tabbaci ne kan hukuncin da babbar kotun Legas ta yanke wa ma'aikatan biyu, Anayo Nwosu da Olajide Oshodi kan samun su da laifin satar N855m.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta sallami wasu ma'aikata daga bakin aiki, ta fadi laifinsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta rahoto Kotun Daukaka Karar, bisa jagorancin Mai shari'a Folasade Ojo, ta yi watsi da daukaka karar da Nwosu da Oshodi suka yi kan hukuncin babbar kotun.

Hukuncin wanda ya samu amincewar sauran alkalan kotun, Mai shari'a Olukayode Bada da Paul Bassi, sun ce hukumar EFCC ta gabatar da kwararan hujjoji.

Hukuncin babbar kotun Legas na farko

A ranar 9 ga watan Disamba, 2019, mai shari'a Jose ta garkame Nwosu da Oshodi kan laifuffuka 15 da suka shafi satar kudi, kamar yadda EFCC ta gabatar mata.

Rahoton Channels TV ya yi nuni da cewa kotun ta haɗa da wani dan Indiya, Ashok Israni da kamfaninsa NULEC Industries a cikin wadanda ta yanke wa hukuncin.

EFCC ta shaidawa kotun cewa wadanda ake tuhuma sun karkatar da N855m mallakin wani kamfani Dozzy Oil and Gas bisa karyar cewa kamfanin NULEC ne zai yi kasuwanci da kudin.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Uba da dansa sun yi taron dangi, sun yiwa matar makwabcinsu duban mutuwa a Ogun

Ma'aikatan bankin sun daukaka kara

Sai dai, jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ma'aikatan bankin da Mr Israni sun daukaka karar wannan hukunci, inda suka nemi adalci a Kotun Daukaka Kara da ke Legas.

A kotun, hukumar EFCC ta sake gabatar da wasu hujjoji da za su tabbatar da tuhumar da take yi wa masu laifin, inda ta ce bai dace shi masu sassauci kan laifin da suka aikata ba.

Kotun Daukaka Kara, ta bi sahun babbar kotu, inda ta yanke wa mutanen hukuncin shekaru 5, bisa samun su da aikata laifuffuka 7 a cikin 15, da suka shafi sata da zamba cikin aminci.

Kotu ta daure likitan bogi a Oyo

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa wata kotun majistare da ke jihar Oyo, ta garkame wani likitan bogi da ake zargin ya yi wa mara lafiya allura ya mutu.

Alkaliyar kotun, Misis A T Oyediji, ta iza keyar likitan mai suna Adegoke Olaoluwa zuwa gidan kaso har sai ta ji daga bakin ofishin kararraki na Oyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel