Badakala: Hukumomin gwamnatin tarayya sun karkatar da N300bn, Majalisa ta dauki mataki akai

Badakala: Hukumomin gwamnatin tarayya sun karkatar da N300bn, Majalisa ta dauki mataki akai

  • Majalisar Dattawa a Najeriya ta umarci wasu hukumomin gwamnatin tarayya da su mayar da wasu kudade asusun gwamnati
  • Rahoton ya bayyana yadda aka zargi hukumomin da karkatar da kudaden ba bisa ka'ida, lamarin da ya kai ga bincike
  • An ruwaito adadin kudaden da kowace ma'aikata ta karkatar, an kuma basu wa'adin kwanaki 60 su gaggauta mayarwa

Daga zauren Majalisa - A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta umarci hukumomin Gwamnatin Tarayya 59 da su mayar da sama da Naira biliyan 300 da ake zargin sun karkatar da su zuwa asusun tarayya, Punch ta ruwaito.

Majalisar ta umarci hukumomin da su dawo da dukkan kudaden da aka kashe ba bisa ka’ida ba daga 2013 zuwa 2015 sannan su aika da su zuwa asusun gwamnatin tarayya cikin kwanaki 60.

Hakan ya biyo bayan rahoton da kwamitin kula da Asusun Gwamnati ya fitar kan rahoton shekara-shekara na gwamnatin na karshen shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Jama’a sun fusata yayin da gwamnatin jihar Taraba ta fara siyar da fom din daukar aiki

KARANTA WANNAN: Dalla-dalla: Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka yanzu

Badakala: Hukumomin gwamnatin Buhari sun karkatar da N300bn, Majalisa ta dauki mataki akai
Shugaban Majalisar Dattijai a Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Adadin kudaden da kowace ma'aikata ta kashe

Sashen Hausa na BBC ya tattaro adadin kudaden da ake zargin hukumomin na gwamnatin tarayya sun karkatar wadanda ake bukata su mayar cikin gaggawa.

Hukumar ta fuskanci cewa hukumar kula da da’ar ma'aikata ta fitar da N995m ba bisa ka'ida ba, ma’aikatar kula da harkokin Neja Delta ta kashe Naira biliyan 1.77 ba a bisa ka'ida ba; Hukumar kula da tashar jiragen ruwa kuma Naira biliyan 68.9 da Dala miliyan 2.3 da Euro196,000.

Hakazalika, shirin inshorar kiwon lafiya ta Najeriya, Naira biliyan 4.35; ofishin kasuwancin jama’a Naira biliyan 8.84; ma’aikatar albarkatun man fetur, Naira miliyan 821.9; hukumar kula da abinci, gudanar da magunguna Naira biliyan 1.88 da bankin Mortgage, Naira miliyan 369.

Shugaban kamitin, sanata Mathew Urhoghide, yace an nemi hukumomin gwamnati 114 a cikin rahoton binciken na 2015, 59 daga ciki an ci gaba da tambayoyi akansu bayan bincike.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka yanzu

Sanata Ibrahim Gobir ya ba da shawarar a aika da rahoton ga hukumar ya ki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa don kwato asusun.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce:

"shawarata ita ce za mu sa ido a kan aiwatar da hakan. Bayan daga kafa na kwana 60 za mu dauki matakin da ya dace na gaba."

KARANTA WANNAN: An sanya dokar takaita zirga-zirga a Katsina saboda shugaba Buhari zai kai ziyara

Da dumi-dumi: Rikici ya barke a zauren majalisa kan batun masana'antar man fetur

A wani labarin, Rikici ya barke a zauren majalisar wakilai a ranar Alhamis kan Dokar Masana’antar Man Fetur (PIB), Daily Trust ta ruwaito.

Rikicin ya fara ne bayan da wasu ‘yan majalisar suka tada jiyoyin wuya kan zargin ragin kaso da aka amince akai ga al’ummomin dake zaune a yankuna masu man fetur.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Majalisar ta riga ta zabi 5% ga al'ummomin dake zaune a yankuna masu man fetur a cikin kudurin PIB a baya yayin da Majalisar Dattawa ta zartar da 3%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel