Sojoji Sun Kashe Dumbin ’Yan Bindiga a Jihohi 2 Na Arewa, Sun Lalata Sansaninsu

Sojoji Sun Kashe Dumbin ’Yan Bindiga a Jihohi 2 Na Arewa, Sun Lalata Sansaninsu

  • Sojoji sun samu nasarar kashe akalla 'yan bindiga 11 a samamen da suka kai jihar Zamfara da Katsina da ke Arewacin Najeriya
  • Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sun yi nasarar tarwatsa sansanin shugaban ƴan bindiga Hassan Yantagwaye a Zamfara
  • Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu a farmakin da sojoji ke ci gaba da kai wa dazuzzukan jihohin Arewa maso Yamma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan bindiga 11 a wani samame da suka kai maboyarsu a jihar Zamfara da Katsina.

Sojoji sun samu nasara a samamen da suka kai Zamfara da Katsina
Sojoji sun tarwatsa sansanin shugaban 'yan bindiga Hassan Yantagwaye a Zamfara. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sojoji sun kashe 'yan biniga a Zamfara

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, ta ce sojojin sun kai samame ne a mabuyar shugaban ’yan bindiga Hassan Yantagwaye da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Uba da dansa sun yi taron dangi, sun yiwa matar makwabcinsu duban mutuwa a Ogun

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Talabijin na AIT ya rahoto rundunar sojin ta ce an kai farmakin ne a ranar 29 ga watan Maris, inda ta kara da cewa sojojin sun lalata maboyar ‘yan ta’addan.

“Yantagwaye da tawagarsa suna da alhakin yin garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci a wasu sassan arewa maso yammacin Najeriya.
"A yayin farmakin, sojoji sun fatattaki 'yan ta'addan a wani artabu da suka yi, inda suka kashe 3 daga cikinsu tare da kwato tarin makamai da alburusai."

- A cewar sanarwar.

Sojoji sun farmaki 'yan bindiga a Katsina

A Katsina, sojojin sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’adda a Shawu Kuka, Shinda, Tafki, Gidan Surajo, da Citakushi a Kabai, karamar hukumar Faskari, a ranar 30 ga Maris.

A yayin gumurzun, sojojin sun kashe 'yan ta'adda takwas tare da kwato "bindigogi uku, kakin soji da dimbin hatsi na sace".

Kara karanta wannan

Kisan 'Yan Sanda a Delta: An kame mutum da ake zargi da yiwa jami'ai kisan gilla

Rundunar ta ce dakarunta sun kwace kullin wiwi 441 a kauyen Molegede da ke karamar hukumar Odeda ta jihar Ogun.

Asibitin Sokoto ya magantu kan Dogo Gide

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani asibitin kwararru da ke jihar Sokoto ya ce ba shi da hannu a yi wa ƙasurgmin dan bindiga Dogo Gide magani.

Hukumar gudanarwar asibitin sun ce Dogo Gide bai je wajensu a lokacin da sojoji suka harbe shi, kuma ba su taba yi wa wani dan ta'adda magani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel