Sojoji Sun Kashe Yan Bindiga 5, Sun Ceto Wasu Dalibai Da Aka Sace a Zamfara

Sojoji Sun Kashe Yan Bindiga 5, Sun Ceto Wasu Dalibai Da Aka Sace a Zamfara

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya karkashin Operatin Hadarin Daji sun halaka yan bindiga biyar a jihar Zamfara
  • Sojojin sun kuma yi nasarar ceto wasu daga cikin daliban da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jami'ar tarayya ta Gusau da ke Sabon Gida
  • Yan bindigar sun kutsa dakin kwanan daliban a safiyar Juma'a, 22 ga watan Satumba, inda suka yi awon gaba da wasunsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Operation HADARIN DAJI da ke yaki da ta'addanci a yankin arewa maso yamma sun yi nasarar halaka yan bindiga biyar a jihar Zamfara.

Kamar yadda Zagazola Makama ya rahoto, sojojin sun kuma ceto wasu daliban jami'ar tarayya ta Gusau da yan bindiga suka yi garkuwa da su a safiyar ranar Juma'a, 22 ga watan Satumba, a garin Sabon Gida da ke jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda 'Yan Bindiga Suka Kutsa 'Hostel' Uku Suka Sace Ɗalibai Mata a Jami'ar Tarayya Ta Gusau

Sojoji sun ceto dalibai a Zamfara
An yi amfani da horon don misali ne kawai. Wadanda ke hoton ba su da alaka da batun da ake magana kansa a rahoton. Hoto: Patrick Meinhardt/AFP.
Asali: Getty Images

Sojoji sun fafata da yan bindigar da suka sace dalibai a Zamfara

Yan bindigar dai sun farmaki garin Sabon Gida da misalin karfe 3:00 na tsakar dare sannan suka yi awon gaba da wasu dalibai na jami'ar tarayya da ke Gusau ciki harda dalibai mata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga bisani sai dakarun sojoji suka bi sahunsu sannan suka yi musayar wuta da yan bindigar inda suka kashe biyar daga cikinsu.

Zafin barin wutan da aka yi masu, ya kuma tilastawa yan bindigar barin wasu daga cikin daliban da suka sace.

Yadda 'Yan Bindiga Suka Shiga Dakunan Kwanan Daliban Jami'ar Tarayya Gusau

Mun dai ji a baya cewa maharan sun kutsa kai cikin gidan kwanan ɗalibai uku kana daga bisani suka kwashe su, suka yi awon gaba da su.

A wani faifan bidiyo da ake yaɗawa a soshiyal midiya, an ga dalibai da dama suna leka ɗakunan abokan karatunsu ko danginsu da harin ya shafa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Tare Da Sace Daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya, Bayanai Sun Fito

An ji wani dalibi da ba a san ko wanene ba a cikin faifan bidiyon yana cewa ‘yan bindigan sun kutsa cikin dakunan kwanan dalibai ta tagogi da silin.

Yan bindiga sun tsere daga dazuzzuka, sun saki wadanda suka sace a Neja

A wani labari na daban, mun ji cewa biyo bayan farmakin da sojoji suka kai a dazuzzukan jihar Neja, yan bindiga da dama sun fara tserewa daga dazuzzuka tare da sakin wasu da aka yi garkuwa da su, rahoton Leadership.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa babu wani kasurgumin dan bindiga da ya ayyana kansa a matsayin gwamna a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel