Jami'an Binance da Aka Tsare Ya Maka NSA da EFCC Kara a Gaban Kotu, Ya Zayyano Bukatunsa

Jami'an Binance da Aka Tsare Ya Maka NSA da EFCC Kara a Gaban Kotu, Ya Zayyano Bukatunsa

  • An shigar da ƙara kan mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) a kotu
  • Babban jami’in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan, ya kai ƙarar NSA da hukumar EFCC bisa zargin tauye masa haƙƙinsa
  • Gambaryan ya ce ana tsare da shi ne saboda gwamnatin Najeriya na neman bayanai daga kamfanin Binance

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban jami’in Binance da ake tsare da shi, Tigran Gambaryan, ya maka mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, da hukumar EFCC ƙara a gaban kotu.

Gambaryan dai ya kai ƙarar hukumar EFCC da NSA ne bisa zargin tauye masa haƙƙinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan ayyukan masu garkuwa da mutane, ya gadi matakin dauka a kansu

Jami'in Binance ya shigar da kara
Gambaryan ya kai karar NSA da EFCC kara gaban kotu Hoto: @officialEFCC/@Naija_PR
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, lauyan Gambaryan, Olujoke Aliyu, ne ya shigar da ƙarar ranar 18 ga watan Maris 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ƙarar da aka gabatar a gaban mai shari'a Inyang Ekwo, Gambaryan ya lissafo buƙatun da yake so a biya masa.

Waɗanne buƙatu jami'in Binance ya nema?

A cikin ƙarar ya nemi kotu ta ayyana cewa tsare shi da ake yi da ƙwace masa fasfo ya saɓa sashe na 35 (1) da (4) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya kuma buƙaci kotun da ta umurci waɗanda yake ƙara da su sake shi sannan su dawo masa da fasfo ɗinsa cikin gaggawa.

Gambaryan ya nemu kotun da ta dakatar da waɗanda ake ƙara daga ci gaba da tsare shi dangane da binciken da suke yi kan kamfanin Binance.

NSA da EFCC ba su halarci zaman ba

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya samo mafita kan hanyar kawo karshen 'yan bindiga a Arewacin Najeriya

A yayin zaman, lauyan Gambaryan ya yi nuni da cewa waɗanda ake ƙarar ba su halarci kotu ba duk da cewa an sanar da su batun ƙarar, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Lauyan ya nemi a ɗage ƙarar domin ba waɗanda ake ƙara damar zuwa su gabatar da bayanansu.

Daga nan sai mai shari'a Ekwo ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar, 8 ga watan Afirilun 2024.

Wani jami'in kamfanin Binance ya tsere

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'in kamfanin kirifto na Binance da ake tsare da shi a Najeriya, ya tsere daga hannun mahukunta.

Nadeem Anjarwalla ya tsere ne bayan jami'an tsaro sun raka shi zuwa wani masallaci domin yin Sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel