Gwamnan Zamfara Ya Samo Mafita Kan Hanyar Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya

Gwamnan Zamfara Ya Samo Mafita Kan Hanyar Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya

  • Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan yadda jihar ta zama cibiyar ƴan bindiga a Arewacin Najeriya
  • Gwamnan ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu inda ya buƙaci a tura ƙarin jami'an sojoji da kayan aiki domin magance matsalar
  • Ya yi nuni da cewa sai an magance matsalar a jihar sannan za a iya kawo ƙarshenta a yankin Arewa baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya roƙi gwamnatin tarayya da ta taimakawa jiharsa domin kawar da ƴan bindiga da satar mutane a Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa a Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya fadi yadda gwamnatin Tinubu za ta yi nasara

Gwamna Dauda ya ba gwamnatin tarayya shawara
Gwamna Dauda Lawal ya bukaci Tinubu ya tura karin jami'an sojoji zuwa Zamfara Hoto: @Mfarees
Asali: Twitter

Gwamna Lawal ya je fadar shugaban ƙasan ne domin ganawa da Shugaba Bola Tinubu kan matsalar rashin tsaro, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawal ya koka kan yadda jihar Zamfara ta zama cibiyar ƴan ta'adda a Arewacin Najeriya.

Ya yi nuni da cewa a cikin ƴan kwanakin nan an samu hare-haren ƴan bindiga da dama a wasu ƙananan hukumomi duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na ganin an kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindigan.

Me Gwamna Dauda ya buƙaci a yi?

Gwamnan ya bayyana cewa jihar ta buƙaci ƙarin jami’an sojoji da kuma kayan aikin da za su ba su damar yin aiki yadda ya kamata domin tunkarar matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar.

A kalamansa:

"An kai hare-hare da dama a wasu ƙananan hukumomin. Ina jin a matsayina na gwamna, ya kamata in sanar da shugaban ƙasa, wanda ya ji daɗin tattaunawar da muka yi, kuma muna neman ƙarin jami’an sojoji da kuma kayan aikin da za su yi amfani da su.

Kara karanta wannan

Halin da Najeriya ke ciki ya sa Tinubu ya hakura da bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa

"A yanzu da na ke magana da ku Zamfara ta zama cibiyar ƴan bindiga kuma idan ba a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a jihar Zamfara ba, ba na tunanin za mu iya magance matsalar a Arewacin Najeriya baki ɗaya."

Ɗaliban jami'ar Gusau sun kuɓuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'adda suka sako dalibai mata tara cikin 21 na jami'ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara bayan shafe tsawon lokaci a tsare.

An sako ɗaliban ne bayan shafe aƙalla watanni tara suna tsare a hannun ƴan bindiga, inda aka yi ta kai-komo kan sakin nasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel