Tinubu Ya Fusata Kan Ayyukan Masu Garkuwa da Mutane, Ya Fadi Matakin Dauka a Kansu

Tinubu Ya Fusata Kan Ayyukan Masu Garkuwa da Mutane, Ya Fadi Matakin Dauka a Kansu

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa waɗanda ke yin garkuwa da mutane ƴan ta’adda ne kuma za a ɗauke su a matsayin hakan
  • Tinubu ya yi nuni da cewa masu garkuwa da mutane matsorata ne da ba za su iya tunkarar sojojin Najeriya ba
  • Shugaban ƙasan ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya yi buɗa baki tare da mambobin ɓangaren shari'a ƙarƙashin jagorancin alƙalin alƙalai na ƙasa, mai shari’a Olukayode Arowola

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Aso-Villa, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da munanan ayyukan ta’addanci da masu garkuwa da mutane ke aikatawa a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ƙasan ya jaddada cewa duk wanda ke da hannu a irin waɗannan munanan laifuffuka dole ne a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya fadi yadda gwamnatin Tinubu za ta yi nasara

Bola Tinubu ya fusata kan masu garkuwa da mutane
Shugaba Tinubu ya ce masu garkuwa da mutane 'yan ta'adda ne Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 26 ga watan Maris, a lokacin buɗa baki a watan Ramadan tare da mambobin ɓangaren shari’a na tarayya, ƙarƙashin jagorancin alƙalin alƙalai na ƙasa (CJN), mai shari’a Olukayode Ariwoola.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Tinubu ya kira su ƴan ta’adda?

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasan Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Talata, Tinubu ya jaddada aniyar gwamnati na kawar da ayyukan ƴan bindiga.

Ya yi nuni da cewa masu yin garkuwa da yara matsorata ne da ba za su iya fuskantar sojojin Najeriya ba.

Fredrick Nwabufo, mataimaki na musamman na Shugaba Tinubu kan hulda da jama’a, ya sanya sanarwar a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Kara karanta wannan

Halin da Najeriya ke ciki ya sa Tinubu ya hakura da bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa

"Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin ƴan ta'adda. Su matsorata ne.
An karya ƙarfinsu. Sun koma neman mutane masu rauni. Suna zuwa makarantu, suna sace yara, suna haifar da rarrabuwar kai.
"Dole ne mu ɗauke su daidai da matsayin ƴan ta'adda domin mu kawar da su, kuma na yi muku alƙawari za mu kawar da su."

Satar yara: Dattawan Arewa sun fusata

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar dattawan Arewa ta fusata kan yadda ake sace yara ɗalibai a yankin.

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Ango Abdullahi, ya gargaɗi gwamnatin Shugaɓa Tinubu da cewa abin ya isa haka kan yadda ake yin garkuwa da ƴan makaranta a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel