Abubuwa Sun Lalacewa Binance, Gwamnati Ta Yi Ƙarar Kamfanin Kan Zargin Laifuffuka 4

Abubuwa Sun Lalacewa Binance, Gwamnati Ta Yi Ƙarar Kamfanin Kan Zargin Laifuffuka 4

  • Gwamnatin Najeriya ta yi karar kamfanin Binance a kan zargin aikata laifuffukan da suka shafi biyan haraji da kuma boye bayanai
  • Gwamnati na zargin Binance da aikata laifuffuka hudu da suka sabawa sashe na 40 na dokar da ta kafa hukumar haraji ta tarayya (FIRS)
  • An saka sunayen Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, manyan jami'an Binance da ke tsare a hannun EFCC a matsayin wadanda ake ƙara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS) ta shigar da tuhumar aikata laifi a kan Binance, fitaccen dandalin hada-hadar kuɗin yanar gizo.

Gwamnati ta yi karar Binance a babbar kotun tarayya Abuja
Gwamnati na tuhumar Binance da aikata laifuffuka a Najeriya Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Binance
Asali: UGC

A karar da hukumar ta shigar gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta nuna cewa tana zargin Binance da aikata laifuffuka hudu.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai mummunan hari a Yobe, sun hallaka soja

Wadanne laifuffuka Binance ya aikata?

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa laifuffukan da ake tuhumar Binance sun haɗa da ƙin biyan harajin VAT, ƙin bayar da bayanan kuɗaɗen shiga don karɓar haraji, ƙin biyan harajin ribar kamfani (CIT).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar FIRS ta kuma zargi Binance da boye sunayen abokan hulɗarta domin ta kare su daga biyan haraji.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a Abuja, FIRS ta ce yanzu ba batun rijistar kamfanin ake ba, ana maganar dokokin harajin Najeriya da kamfanin Binance ya karya.

Gwamnati ta yi karar jami'an Binance

A cewar sanarwar FIRS:

"Gwamnati na zargin cewa Binance ta ƙi yin rijistar kamfaninta ne domin ta gujewa biyan haraji, kuma ta karya dokokin harajin ƙasar.
"Daya daga cikin tuhumar da muke yi wa kamfanin shi ne gaza biyan kudaden haraji na bangarori daban daban, wanda ya sabawa sashe na 40 na dokar da ta kafa hukumar FIRS a 2007."

Kara karanta wannan

Kebbi: Barayin shinkafa sun farmaki hukumar Kwastam, sun tafka mummunan barna

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, hukumar ta saka sunayen Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, manyan jami'an Binance da ke tsare a hannun EFCC a matsayin wadanda ake ƙara na biyu da na uku.

Hukumar ta kuma jaddada cewa dole ne a tabbatar an yi amfani da dokokin haraji wajen magance laifuffukan da ake yi a kasuwar cryptocurrency.

Jami'in Binance da aka tsare ya tsere

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa daya daga cikin jami'an kamfanin Binance da ke tsare a hannun hukumar EFCC ya tsere.

Jami'in mai suna Nadeem Anjarwalla, ya tsere ne a lokacin da ya nemi izinin zuwa masallacin Juma'a, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel