Halin Kunci: Gwamnan APC Zai Rage Farashin Kayan Abinci da 25% Yayin da Aka Fara Azumi

Halin Kunci: Gwamnan APC Zai Rage Farashin Kayan Abinci da 25% Yayin da Aka Fara Azumi

  • Yayin ake cikin wani irin mawuyacin hali a fadin Najeriya, Gwamnan Legas zai kawo hanyar rage farashin kaya a jiharsa
  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana shirin rage farashin kayan abinci a jihar da kaso 25 domin ya saukakawa al’umma
  • Wannan mataki na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake cikin wani irin hali na tsadar rayuwa tare da fara azumin watan Ramadan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya shirya rage farashin kayayyaki a jiharsa yayin da ake halin kunci.

Mai girma Sanwo-Olu zai rage farashin kayan ne da kaso 25 ta yadda jama’a za su samu saukin siyan kayan abinci cikin walwala.

Kara karanta wannan

Arewa ta barke da murna bayan ware $1.3bn kan aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi

Gwamnan APC zai farantawa al'ummar jiharsa rai kan rage farashin kayan abinci
Gwamna Sanwo-Olu ya dauki matakin ne domin saukakawa al'ummar jihar Legas. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Getty Images

Matakin Sanwo-Olu kan tsadar abinci a Legas

Wannan na kunshe ne a cikin wata wallafawa da gwamnatin jihar ta yi a shafinta na X a safiyar yau Alhamis 14 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki da gwamnatin za ta dauka ba iya rage radadin wahala zai yi zai kuma kara aminci a tsakanin al’ummar jihar da gwamnati wurin inganta rayuwarsu.

Wannan mataki na Gwamna Sanwo-Olu zai yi matukar tasiri wurin tabbatar da samun sauki musamman ga 'yan jihar yayin da suke kokawa kan tsadar abinci.

Tasirin matakin da Sanwo-Olu ya dauka

Yayin da ‘yan jihar ke nuna jin dadi kan wannan mataki na gwamnatin jihar, mazauna Legas sun kuma bukaci samar da kamfanin bunkasa harkokin noma a jihar.

Sun tabbatar da cewa samar da cibiya ta bunkasa harkokin noman zai tabbatar da samun ragi a farashin kayan da kuma isa inda ya kamata abincin ya je.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba gwamnonin jihohi sabon umarni kan mafi karancin albashi, bayanai sun fito

Matakin na gwamnan na zuwa a dai-dai lokacin da ake shan fama da tsadar rayuwa a fadin Najeriya.

Gwamna Aliyu ya ba da goron azumi

A baya, mun ruwaito muku cewa gwamna jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya gwangwaje ‘yan jihar da rabin albashinsu kyauta.

Gwamna Aliyu ya dauki wannan matakin ne domin tallafawa ma’aikatan jihar yin azumi cikin walwala da farin ciki.

Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin wani mawuyacin hali na matsain tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel