Gobara Ta Tashi a Kasuwar Wuse, Babban Birnin Tarayya Abuja, Ta Yi Barna

Gobara Ta Tashi a Kasuwar Wuse, Babban Birnin Tarayya Abuja, Ta Yi Barna

  • Wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar Wuse, babban birnin tarayya Abuja, inda ta kone shaguna da motocin mutane da ke ajiye
  • Ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba har zuwa rubuta wannan labari, amma lamarin ya kawo karshen harkokin kasuwanci na yau
  • Ana fargabar wasu fusatattun matasa ne suka cinnawa wani bangare na babbar kasuwar wuta saboda kashe wani matashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shahararriyar kasuwar Wuse da ke tsakiyar Abuja, babban birnin tarayya, ta kone kurmus a yammacin ranar Talata.

Ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba amma lamarin ya kawo karshen harkokin kasuwancin yau a yankin kasuwar.

Gobara ta tashi a kasuwar Wuse, Abuja
Gobara ta babbake motoci a kasuwar Wuse, Abuja. Hoto: @Fedfireng
Asali: Facebook

Channels TV ta ruwaito cewa barkewar gobarar ta haifar da rufe dukkanin hanyoyin da ke kai wa zuwa kasuwar yayin da aka ga mutane suna gudun kai dauki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari kasuwa, sun kashe mutane da dama ana murnar zuwan Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin matasa da saka wuta

‘Yan sandan da suka isa kasuwar, sun tare kofar shiga bangaren da gobarar ta tashi domin hana jama’a aikata wani aikin laifin.

Tuni dai wasu motocin da ke ajiye a wurin ajiye motoci na kasuwar suka kone kurmus yayin da jami’an kashe gobara suka fara aikin ceto.

Rahoton Daily Trust ya yi nuni da cewa wasu fusatattun matasa ne suka cinnawa wani bangare na babbar kasuwar wuta saboda kashe wani matashi dan shekara 17 mai suna Musa.

Hukumar AMML ta tabbatar da gobarar

Wani babban jami’in hukumar kula da kasuwannin Abuja (AMML) wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Da yake tabbatar da faruwar gobarar, jami’in hulda da jama’a na hukumar ta AMML, Innocent Amaechina, ya ce jami’an hukumar kashe gobara da ‘yan sanda sun killace yankin.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Ba a dai bayyana adadin mutanen da suka jikkata sakamakon turmutsitsin da aka yi yayin da mutane suka rinka neman hanyoyin fita daga kasuwar.

Farashin kayan abinci ya karu a Abuja

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda mazauna Abuja suka koka kan yadda 'yan kasuwa suka kara kudin kayan abinci a kasuwannin babban birnin tarayyar kasar.

An zargi an yi karin kudin ne yayin da aka shigo watan azumin Ramadana, wanda mazauna garin ke ganin ya zama kamar al'ada a wajen wasu 'yan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel