Matatar Man Fatakwal Za Ta Fara Aiki Yayin da Najeriya Ke Shirin Daina Shigo da Fetur

Matatar Man Fatakwal Za Ta Fara Aiki Yayin da Najeriya Ke Shirin Daina Shigo da Fetur

  • Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce nan da makonni biyu matatar mai ta garin Fatakwal a Ribas za ta fara aikin tace mai
  • Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan a wata ganawa da wani kwamitin majalisar dattawa a birnin tarayya Abuja
  • Kyari ya kuma yi alkawarin cewa Najeriya za ta daina shigo da fetur daga shekarar 2024, biyo bayan sauran matatun kasar da za a farfado da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya ce nan da mako biyu matatar mai ta Fatakwal, da ke jihar Rivers za ta fara aiki.

Kyari ya ce ya zuwa yanzu matatar ta karbi ganga 450,000 na danyen mai domin tacewa bayan da aka kammala gyaran matatar a Disambar 2023.

Kara karanta wannan

An cafke babban lauya da zargin kin biyan 'yar gidan magajiya bayan sun gama lalata

Matatar man Fatakwal za ta fara aiki
NNPCL ta ce gwamnati ta dauki matakan daina shigo da fetur. Hoto: Mele Kyari
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Kyari ya bayyana hakan ne a wata ganawa da kwamitin majalisar dattawa da ke bincike kan yadda ake kula da matatun mai (TAM) na kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu farfado da matatun mai" - NNPCL

Da ya ke jawabi ga mambobin kwamitin, Kyari ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ba da hadin kai wajen ganin kamfanin ya cimma muradunsa na wadatuwar fetur a kasar.

Kyari ya ba 'yan Najeriya tabbacin cewa za a bude matatar mai ta Fatakwal da sauran matatu kamar yadda aka tsara ba tare da jinkiri ba.

"Za mu tabbatar mun cika dukkanin alkawurran da muka dauka na farfaɗo da matatun man Najeriya. Yanzu zamu fara da matatar Fatakwal, wacce aka kammala komai a Disambar 2023.
"Yanzu haka ma akwai danyen mai da matatar ta karba don tacewa, nan da makonni biyu za ta fara aiki gadan-gadan."

Kara karanta wannan

Duk da gwamnati ta dauki mataki, farashin gas din girki ya sake lulawa har ya haura N1300

Shirin NNPCL a kan sauran matatun mai

Dangane da farfaɗo da sauran matatu, jaridar Tribune Online ta ruwaito Kyari na cewa:

"A bangaren matatar Warri, zuwa yanzu mun kammala gyaran karafa, muna binciken wasu bangarorin na ta domin tabbatar da cewa za ta iya yin aiki nan gaba.
"Zuwa Disambar wannan shekarar matatar Kaduna za ta fara aiki, amma har yanzu ba mu kai wannan gabar ba. Muna fatan za mu kammala komai a kan lokaci."

2024 kamfanin NNPCL zai daina shigo da fetur

Gidan talabijin na Arise ya ruwaito cewa, Mele Kyari ya lashi takobin kawo karshen shigo da fetur a Najeriya a wannan shekara ta 2024.

Kyari ya bayyana hakan ne a Abuja, a wani taron kaddamar da wasu littattafai biyu da tsohon shugaban kamfanin mai na NOC, Farfesa Billy Okoye ya wallafa.

Kyari ya bugi kirji da cewa yanzu Najeriya na da wadatattun matatun mai da za su ishi ƙasar wajen samar da fetur, iskar gas da sauran su.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da makiyaya ne ke jawo wahalhalun da ake sha a Najeriya, inji fasto Ayodele

"Za mu kawo karshen wahalar fetur" - NNPCL

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce nan da shekarar 10 zai kawo karshen wahalar man fetur a Najeriya.

Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ya ce kawo karshen wahalar fetur ba karamin aiki ba ne sabanin yadda wasu ke tunani, yana mai cewa NNPCL ya dauki matakai don cimma hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel