Tinubu Na Fuskantar Sabuwar Matsala Yayin Da ’Yan Fansho Ke Shirin Fita Zanga-Zanga Tsirara

Tinubu Na Fuskantar Sabuwar Matsala Yayin Da ’Yan Fansho Ke Shirin Fita Zanga-Zanga Tsirara

  • Shugaba Bola Tinubu na fuskantar wata barazana daga kungiyar 'yan fansho, wadanda suka ce za su yi zanga-zanga tsirara a fadin kasar
  • Sunday Omezi, shugaban kungiyar 'yan fanshon, ya ce har yanzu 'yan fansho ba su samu karin alawus ba kamar yadda gwamnati ta alkawarta
  • Yayin da Omezi ya yi nuni kan karatowar wa'adin daina biyan karin albashin, kungiyar 'yan fansho ta ce akwai masu daukar N1,500 a wata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Manyan 'yan kasa, karkashin kungiyar tsofaffin ma'aikatan gwamnati (FCSP), wadda ke karkashin kungiyar fansho ta NUP, sun ce za su gudanar da zanga-zanga.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito a ranar 14 ga watan Maris, 'yan fanshon sun yanke wannan shawarar ne bayan gazawar gwamnati na biyansu karin kudin fansho.

Kara karanta wannan

Arewa ta barke da murna bayan ware $1.3bn kan aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi

Yan fansho za su fita zanga-zanga
Yan fansho sun koka kan yadda gwamnati ta yi watsi da su a karin albashi. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tsofaffin ma'aikatan sun yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta tuna cewa ana fama da yunwa da tsadar rayuwa a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidan talabijin na AIT ya fitar da rahoto cewa 'yan fanshon sun lashi takobin fita zanga-zaga tsirara ma damar gwamnati ba ta saurari kokensu ba.

"Ba mu samu karin albashi ba" - Omezi

Da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, Sunday Omezi, shugaban kungiyar FCSP, ya ce:

"Abun takaici ne ace har yanzu gwamnati ta gaza biyan karin N25,000 da ta yi wa 'yan fansho alkawari.
"Muna matukar takaicin yadda za ace ko mutum daya ba a turawa wadannan kudade ba, ga shi har wa'adin watanni shida da aka diba ya kusa karewa."

Da aka tambaye shi ko kungiyarsu za ta yi zanga-zanga kan lamarin, Omezi ya ce:

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba gwamnonin jihohi sabon umarni kan mafi karancin albashi, bayanai sun fito

"Muna fatan ba za ta kai mu ga yin zanga-zanga ba. Wannan ne dalilin ganawa da manema labarai, amma idan har ba a biya mana bukata ba, to ba shakka za mu mamaye ƙasar."

"'Yan fansho na karbar N1,500 a wata" - NUP

Dangane da wannan lamari, kungiyar 'yan fansho ta NUP ta koka kan cewa har yanzu akwai tsofaffin ma'aikata da ake biya N1,500 a wata matsayin kudin fansho.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta yi duban gaggawa kan wannan lamari domin kara yawan kudin ga tsofaffin ma'aikata.

Haka kuma, NUP ta reshen Kudu maso Kudu da ke da ofis a Uyo, jihar Akwa Ibom, ta zayyana irin wahalhalun da mambobinta ke fuskanta sakamakon tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar.

Jihohi 12 da ke biyan ma'aikata karin albashi

A safiyar yau Alhamis ne Legit Hausa ta tattaro bayani kan jerin jihohin Najeriya 12 da ke biyan ma'aikatansu karin albashi.

A yayin da wasu jihohi ke biyan N35,000 ga ma'aikatan, wasu kuma na biyan N10,000 ne. Karin kudin an yi shi don rage wa ma'aikata radadin tsadar rayuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel