'Dan Najeriya Ya Shiga Tasku, Matarsa Ta Sake Shi Bayan Ya Kashe Miliyoyi a kanta

'Dan Najeriya Ya Shiga Tasku, Matarsa Ta Sake Shi Bayan Ya Kashe Miliyoyi a kanta

  • Wani 'dan Najeriya ya cika da mamaki da bugun zuciya yayin da matarsa ta umurce shi da ya fice daga gidan aurensu
  • Yayin da yake tattara kayansa, mutumin ya sanya daya daga cikin yaransa ya yi masa hoto yayin da yake korafi kan abin da matar ta yi
  • Ya ce ya kashe fiye da Yuro 24k (naira miliyan 47) wajen daukar nauyin karatun matar tasa, katsam sai ta saka masa da irin haka a turai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani 'dan Najeriya da aurensa ya samu tangarda ya shawarci 'yan uwansa maza da kada su kuskura su kai matayensu kasar waje.

Mutumin wanda zuciyarsa ta bugu ya bayar da shawar ne yayin da yake tattara kayansa daga gidansa a turai bayan matarsa ta nemi lallai ya fice daga gidan.

Kara karanta wannan

Wani 'dan Najeriya ya girgiza intanet yayin da ya ci miliyan 60 a caca da N798

Dan Najeriya ya koka bayan matarsa ta kore shi daga gida
'Dan Najeriya ya koka da sharrin mata Hoto: Thinkstock, Dougal Waters
Asali: Getty Images

@portharcurticons_ ya yada wani bidiyo da daya daga cikin yaransa ya dauka a dandalin TikTok. Bidiyon na dauke da abin da shi yace ya faru ta bangarensa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya sayar da filaye don daukar nauyin karatun matar

Mutumin ya koka cewa matarsa ta kira masa 'yan doka, tana mai ikirarin cewa ya yi barazana ga rayuwarta.

Da yake korafi, ya tuna da yadda ya tura ta turai domin ta karanci ilmin lauya sannan ya nauyin karatun daga abin da ya samu bayan ya sayar da filayensa.

"Na tura ki turai don ki zo ki yi karatun lauya. Na yi maki komai. Na siyar filaye na don ki je makaranta amma wannan ne abin da za ki iya yi don ki saka mani.
"Kin je kin kira mani 'yan doka, cewa ina barazana ga rayuwarki."

Kara karanta wannan

Bayan shekaru da dama, magidanci ya gano ba shine mahaifin 'diyarsa mai shekaru 18 ba

Ya gargadi maza kan kai matayensu turai

Ya caccake ta, yana mai cewa ya kashe Yuro 24k (sama da naira miliyan 47) wajen kai ta makaranta sannan ya roki Allah ya saka masa.

"Kuskure mafi muni da za ka yi shine tura matarka turai. Ya 'dan uwana ka ji ni, idan kana da niyar kai matarka turai, to ka sauya tunanin yanzun nan ko kuma ka ji a jikinka," ya shawarci maza.

Da take tsaye kan bakarta, matar bata karyata ikirarinsa ba sannan ta dunga yi masa ihun ya kwashe kayansa daga gidan.

Da take daga murya a kasan bidiyon, ta ce komawa turai da ta yi ya sa kanta ya waye.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan lamarin ma'auratan

@mosesolumuyiwawhetode ya ce:

"Kuskuren da muke yi shi ne cewa za mu iya canja dabi'ar mutum."

Muhammad Usman ya ce:

"Na kawo matata turai sannan ta aika ni gidan yari, ina gidan yari tsawon shekaru 10 kenan. har yanzu ina a kurkuku."

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya karya gwiwar Sheikh Daurawa, ya yi murabus daga shugabancin Hisbah

expensive ta ce:

"Don Allah ku sani ba dukka mata ne suka taru suka zama daya ba a bangare na sanin daga gidan da na fito mijina na iya kai ni turai zan kasance mai biyayya har abada."

Kotu ta raba auren shekaru 14

A wani labari na daban, mun ji cewa a ranar Talata ne wata kotu da ke Kubwa, Abuja, ta raba auren wata mata mai suna Salamatu Halilu da mijinta Ibrahim Sumaila bayan shafe shekaru 14 suna tare.

Alkalin kotun, Muhammad Wakili, ya raba auren ne kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, bayan bukatar da Salamatu ta yi na neman saki bisa dalilin rashin soyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel