Wani ‘Dan Najeriya Ya Girgiza Intanet Yayin da Ya Ci Miliyan 60 a Caca Da N798

Wani ‘Dan Najeriya Ya Girgiza Intanet Yayin da Ya Ci Miliyan 60 a Caca Da N798

  • Masu amfani da dandalin soshiyal midiya sun yi ta cece-kuce bayan wani mutumi ya sanar da cin zunzurutun kudi har naira miliyan 60 a caca
  • Mutumin wanda ya buga cacar da kafar dama ya samu kudi masu yawan gaske bayan ya saka N798 kacal
  • 'Yan Najeriya da dama sun cika da mamakin yadda aka yi ya yi nasara, yayin da wasu kuma roke shi da ya basu satar amsa a wasannin gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani 'dan Najeriya, @_spiriituaL, ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya ci naira miliyan 60 a caca.

@_spiriituaL ya garzaya shafinsa na X don baje kolin tikitin nasarar da ya samu, yana mai bayyana cewa da N789 kacal ya cinye cacar.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru da dama, magidanci ya gano ba shine mahaifin 'diyarsa mai shekaru 18 ba

Matashi ya taki babban sa'a a caca
Wani ‘Dan Najeriya Ya Girgiza Intanet Yayin da Ya Ci Miliyan 60 a Caca Da N798 Hoto: @_spiriituaL
Asali: Twitter

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, an samu mutum sama da miliyan daya da suka duba wannan nasara tasa yayin da wasu da dama suka sha mamaki kan nasarar da ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama sun so sanin sirrin wannan gagarumar nasarar da ya samu. Ba shi ne mutum na farko da ya fara samun irin wannan nasara ba a gidan caca ba domin dai wani mutum ya ci naira miliyan 72.7 a 2022.

Ga wallafarsa a kasa:

Jama'a sun yi martani

@OKWYtycoon ya ce:

"Dan uwa za ka iya shigar da ni kungiyarka ka caje ni zan biya, baya ga haka ina caca mai tsawo nima. Baaba dole na samu a caca fa."

@Ola_Daniels1 ya ce:

"Dan Allah fa @_spiriituaL da alama zan shiga ajinka don ka koyar da ni darasi."

Kara karanta wannan

Dangi sun shiga makoki yayin da tuwo ya kashe mutum, aka kwantar da 4 a asibiti

@Ashabul_Jannaah ya ce:

"Zan fara buga caca daga yau, wannan gagarumi ne."

Dan caca zai tallafawa wani dalibi

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani dan Najeriya, wanda aka fi sani da Mr Bayo, yana shirin taimakon wani matashin dalibi wanda ya yi asarar kudin makarantarsa a caca.

Legit Hausa ta rahoto yadda wani dalibi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya ba da labarin yadda ya rasa kudin makarantarsa a harkar caca.

Rubutun nasa wanda ya goge a yanzu ya dauki hankalin Mr Bayo, wanda ya ci naira miliyan 102 a caca yan kwanaki da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel