“Na Wahala da Shi”: Budurwa ta Fashe da Kuka Yayin da Saurayinta Na Shekaru 7 Ya Auri Wata

“Na Wahala da Shi”: Budurwa ta Fashe da Kuka Yayin da Saurayinta Na Shekaru 7 Ya Auri Wata

  • Wata budurwa yar Najeriya ta samu karayar zuciya bayan masoyinta na shekaru bakwai ya nuna mata halin yan maza
  • Ta gano cewa saurayin nata ya auri wata daban inda ta garzaya dandalin soshiyal midiya domin baje kolin halin da take ciki
  • Yayin da wasu masu amfani da soshiyal midiya suka tausaya mata, wasu sun cika da al'ajabin dalilin shafe shekaru bakwai ana soyayya ba tare da wani shiri ba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar budurwa ta koka a soshiyal midiya bayan ta gano cewa saurayinta ya auri wata daban.

A cikin wani bidiyon TikTok, @queensglownaturals ta bayyana cewa sun shafe shekaru bakwai tare, sannan ta bayyana cewa ta sha wahala da shi.

Kara karanta wannan

Zo ka jaraba: Bature na neman yan Najeriya da za su iya yin minti 3 suna kuka, zai biya daloli

Matashiya ta koka yayin da saurayinta ya auri wata daban
“Na Wahala da Shi”: Budurwa ta Fashe da Kuka Yayin da Saurayinta Na Shekaru 7 Ya Auri Wata Hoto: @queensglownaturals
Asali: TikTok

Tana ta sharban kuka a bidiyon yayin da ta mayar da hankali kan kamarar. Ta tuna yadda ta bata lokacinta, karfinta harma da zama da yunwa tare da shi yayin da take tallafawa aikinsa na barkwanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta rubuta:

"Na sha wahala tare da shi cikin ruwa da rana muna bidiyon barkwanci da zama da yunwa, na sadaukar da lokaci na da karfina kawai sai ya watsar da ni ya auri wata daban, maza basu da tabbass Allah zai hukunta shi.."

Jama'a sun yi martani

Bidiyonta ya haifar da martani daban-daban daga wajen masu amfani da soshiyal midiya.

goldzera226 ta ce:

"Irin tsinuwar da zan yi masa.
"Hatta ga mutanen kauyensa sai sun san mutum ya tsine masa."

Favour Jacktor ta ce:

"Shiyasa idan ba zan iya ba da bayanin soyayyata a shekara daya ba yar uwa zan hakura ba zan yarda wani ya yi amfani da ni wajen gwaji ba."

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya maida martani kan dakatar da ministar jin kai, ya aike da sako ga Tinubu

KINGWHALES ya ce:

"Yar'uwa ya danganta da yadda kika yi masa a shekaru 7 ba wai batun shekaru 7 bane kawai."

Mazaunin turai na neman gwanin kuka

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiya yar Najeriya, Olaedo Chioma Irene, ta bayyana cewa wani abokinta a kasar Birtaniya yana bukatar wani da zai iya yin bidiyo mai tsawon mintuna uku yana kuka.

Ta ce mutumin na so ya yi amfani da bidiyon kukan ne a wakokinsa sannan ta bukaci duk wanda ke sha'awar abun ya tura bidiyonsa ta shafinta na WhatsApp.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel