Matashiya Ta Yi Baiko da Saurayinta Bature Bayan Ta Rabu da Mijin da Ya Kai Ta Turai

Matashiya Ta Yi Baiko da Saurayinta Bature Bayan Ta Rabu da Mijin da Ya Kai Ta Turai

  • Wata mata ta nuna godiya ga tsohon mijinta yayin da ta sanar da yin baiko tsakaninta da sabon sahibinta
  • Matar ta baje kolin sabon sahibin nata da kuma irin zoben alkawarin da ya bata a dandalin TikTok kuma tuni bidiyon ya yadu
  • Ta magantu kan yadda lokaci mafi muni a rayuwarta ya zame mata alkhairi sannan ta yi godiya ga Allah kan sauyin da ta samu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata mata mai suna @jeanchronicles, ta yi murnar samun sabon saurayi bayan sun yi baiko da sahibinta da ta hadu da shi a turai.

@jeanchronicles ta yada hoton da ta dauka da tsohon mijinta da fuskarsa a rufe. Ta gode masa kan yadda ya dauke ta ya kai ta turai, wanda a nan ne ta samu abokin rayuwa.

Kara karanta wannan

Sadiya Marshall ta kunyata, ta janye kalamanta kan Layla da ta bar hannun DSS

Bakar fata ta hadu da bature a turai
Matashiya Ta Yi Baiko da Saurayinta Bature Bayan Ta Rabu da Mijin da Ya Kai Ta Turai Hoto: @jeanchronicles
Asali: TikTok

Ta jinjinawa sabon sahibinta

A wata wallafa da ta yi a TikTok, @jeanchronicles ta yada hotunan da ta yi da sabon sahibin nata da kuma diyarta inda ta yi zantuka masu dadi a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da take magana kan sabon sahibin nata, ta ce ta samu wanda ke so da mutunta ta. Ta jinjina masa kan karfafa mata gwiwar barin aurenta na baya da kuma zamowa uba ga 'yarta.

"Lokaci mafi muni a rayuwata ya rikida ya zama alkhairi, abin da makiyi ya yi na mugunta ya rikida ya zama alkhairi gareni. Na dauki kaina bayan an yi watsi da ni sannan na sake gina rayuwata, Allah ya mayar da hawayena zuwa na farin ciki," ta rubuta a TikTok.

Ta rufe sashin sharhi bayan wallafar tata, don hana mutane bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin.

Kara karanta wannan

"An hada miliyan 17": Yan Najeriya sun hadawa wani dattijo da ke aikin kera bulo kudade

A wani rubutun nata, matar ta jinjinawa kanta kan karfin halin da ta yi na kin karbar shawarwarin 'yan uwa, wadanda ke son ta ci gaba da rayuwar aure mai kunci.

Mata ta kama miji yana tarayya da mahaifiyarta

A wani labari mun ji cewa rikici ya barke tsakanin wasu iyali a jihar Nasarawa sakamakon ikirarin da wata matar aure ta yi cewa mijinta ya ci amanarta ta hanyar kwanciya da mahaifiyarta.

Matar mai suna Doris ta ce danta mai shekaru shida ne ya tona asirin mijin nata mai shekaru 46 da mahaifiyarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel