Shugaba Tinubu Ya Fito Ya Fadi Gaskiyar Halin da Tattalin Arzikin Kasar Nan Ke Ciki

Shugaba Tinubu Ya Fito Ya Fadi Gaskiyar Halin da Tattalin Arzikin Kasar Nan Ke Ciki

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai yarda da batun cewa tattalin arziƙin Najeriya na cikin wani mawuyacin hali ba
  • Shugaban ƙasan ya yi nuni da cewa tattalin arziƙin ƙasar nan bai kai matsayin da za a cire tsammani a kansa ba
  • Ya bayar da tabbacin cewa manufofinsa da sauran matakan da gwamnatinsa ke ɗauka za su dawo da tattalin arziƙin ƙasar nan kan turba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Talata, 5 ga watan Maris, ya yi magana kan halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki.

Shugaban ƙasan ya ce tattalin arziƙin ƙasar nan ba ya cikin ƙaƙanikayi, yana mai jaddada cewa halin da ake ciki yanzu bai wuce a gyara shi ba, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: An samu hanyar da za a kawo karshen 'yan bindiga a Najeriya

Tinubu ya magantu kan tattalin arzikin Najeriya
Shugaba Tinubu ya ce tattalin arzikin Najeriya baya cikin kakanikayi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ƙasan dai yana adawa da iƙirarin da ake yi na cewa tattalin arziƙin ƙasar nan ya shiga cikin wani mawuyacin hali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tinubu ya ce kan tattalin arzikin Najeriya?

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne dai yayin da yake jawabi a wajen taron bayar da lambar yabo na shekara-shekara na 'Leadership 2023 Conference and Awards' karo na 16 wanda aka gudanar a otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Bello, shi ne ya wakilci shugaban ƙasan a wajen taron.

A kalamansa:

"Ya kamata na fara da ƙalubalantar ra'ayin cewa tattalin arzikin Najeriya na cikin ƙunci. Matsi yana nuna gazawa, kasancewa cikin neman ɗauki kan abin da ba mu da iko akai. Amma ba haka lamarin yake ba.
"Muna cikin lokuta masu wahala, babu shakka, amma waɗannan lokutan kuma sun samar da damarmakin da ba a taɓa ganin irinsu ba, don sake saita hanya da gina sabon tattalin arziƙi mai ɗorewa, wanda ya kaucewa nemo bashi da almubazzaranci da aka saba yi a baya

Kara karanta wannan

Binance: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya goyi bayan matakin da Shugaba Tinubu ya dauka

Shugaban ƙasan ya kuma yi nuni da cewa manufofinsa da sauran matakan da gwamnatinsa ke ɗauka na kan turba, rahoton PM News ya tabbatar.

FG Ta Fadi Dalilin Tsadar Abinci

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan noma da samar da abinci ya faɗi dalilin da ya sa ake wahalar abinci a Najeriya.

Abubakar Kyari ya bayyana cewa safarar kayan abinci da ake yi daga Najeriya xuwa ƙasashe makwabta ne, ke jawo ƙaranci abinci a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel