Juyin mulki: Sojoji Sun Yi Albishir Ga 'Yan Najeriya Kan Jita-jitar da Ake Yadawa

Juyin mulki: Sojoji Sun Yi Albishir Ga 'Yan Najeriya Kan Jita-jitar da Ake Yadawa

  • Rundunar sojojin Najeriya ta sake tabbatar da kokarinta wurin kare martabar tsarin dimukradiyya a kasar nan
  • Rundunar ta ce tun da Najeriya ta zabi tsarin dimukradiyya dole za ta kare martabarta a matsayinta na mai tsaro
  • Hafsan sojin kasar, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja shi ya bayyana haka a yau Talata 5 fa watan Maris a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta bayyana himmatuwarta wurin tabbatar da dimukradiyya a kasar.

Rundunar ta ce za ta yi duk mai yiyuwa domiin tabbatar da dimukradiyya ta zauna da gindinta a Najeriya.

Rundunar soji ta yi martani kan tabbatar da dimukradiyya a Najeriya
Sojoji sun dauki alkawarin kare martabar dimukradiyya a Najeriya. Hoto: Bola Tinubu, @HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Martanin sojin Najeriya kan dimukradiyya

Hafsan sojin kasar, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja shi ya bayyana haka a yau Talata 5 fa watan Maris a Abuja, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaban Kwastam ya bayyana a gaban majalisa, ya faɗi gaskiya kan siyar da kayan abinci ga talakawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lagbaja ya ce aikin rundunar ne ta kare martabar dimukradiyya a kasar domin haka babu dalili da za ta kawo cikas a tsarin.

Taoreed ya ce rundunar wani bangare ne a dimukradiyya kuma hakkin 'yan siyasa ne su yi jagoranci su kuma sojoji su yi aikinsu kamar yadda doka ta ce.

Janar ya shawarci rundunar sojin Najeriya

Hafsun ya bukaci jami'an rundunar da su yi aiki tukuru yayin da suke gudanar da aikinsu na tsaron kasa, cewar Daily Post.

"Zan yi amfani da wannan dama domin tabbatar maku da cewa muna tare da tsarin dimukradiyya.
"Za mu ci gaba da kare martabar dimukradiyya tun da Najeriya ta zabe shi a matsayin tsarin mulki.
"Mu wani bangare ne na dimukradiyya, za mu ci gaba da kare ta ba wai neman ruguza ta ba."

- Taoreed Lagbaja

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke shugaban ƴan bindiga da tawagarsa ta addabi jihar Katsina

Wannan martani na zuwa ne yayin da wasu 'yan ke kiran a yi juyin mulki saboda halin kunci da rashin ingantacciyar rayuwa.

Sojoji sun gargadi masu kiran juyin mulki

Kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta tura zazzafan gargadi kan masu kiran juyin mulki a kasar.

Rundunar ta ce duk masu kiran juyin mulkin ba su da kishin kasa kuma za su fuskanci hukunci idan aka damke su.

Wannan na zuwa ne yayin wasu daga cikin 'yan kasar ke fatan a yi juyin mulki a kasar saboda halin kunci da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel